1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar buƙatar kawo ƙarshen rikicin Siriya

May 10, 2012

Kofi Annan ya jaddada buƙatar ɓangarorin dake rikici a Siriya su kawo ƙarshren zubar da jini.

In this photo released by the Syrian official news agency SANA, flames and smoke raise from burning cars after two bombs exploded, at Qazaz neighborhood in Damascus, Syria, on Thursday May 10, 2012. Two large explosions ripped through the Syrian capital Thursday, heavily damaging a military intelligence building and leaving blood and human remains in the streets. (Foto:SANA/AP/dapd)
Hoto: AP

Babban mai shiga tsakani na ƙasa da ƙasa a rikicin Siriya Kofi Annan ya yi Allah wadai da wasu tagwayen bama-baman da suka tashi a birnin Damascus a wannan Alhamis, kana ya buƙaci dakarun Siriya da 'yan tawayen ƙasar da su kawo ƙarshen zubar da jini - kamar yanda suka amince a yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a ƙasar kimanin wata ɗaya kenan. Annan, wanda ke shiga tsakani a madadin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙungiyar ƙasashen Larabawa yana ta fafutukar ci gaba da yin aiki da shirin samar da zaman lafiya, mai rukunai shidda ne domin hana ƙasar ta Siriya faɗawa cikin yaƙin basasa. Hakanan shi ma shugaban tawagar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar ta Siriya Manjo Janar Robert Mood ya nuna alhinin sa tare da jajantawa Iyalai da kuma waɗanda hatsarin ya rutsa da su:

"Ya ce saƙo na ga ɗaukacin waɗanda suka ruruta wannan rikicin shi ne su kwana da sanin cewar wannan ba ita ce mafita ba ga matsalar. Saboda haka muna buƙatar 'yan Siriya da kuma al'ummomin ƙasa da ƙasa da su bayar da gudummowar su wajen kawo ƙarshen wahalhalun da mata da ƙananan yara da kuma ɗaukacin 'yan Siriya ke fama da su."

A yanzu dai ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Siriya ta tabbatar da cewar wasu 'yan ƙunar baƙin wake ne suka ƙaddamar da tagwayen hare-haren, waɗanda ta ce sun janyo mutuwar aƙalla mutane 55 a yayin da wasu 372 kuma suka sami rauni tare da lalata ginin hukumar leƙen asirin ƙasar ta Siriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman