Sabuwar cibiyar yaki da cutar Ebola.
July 11, 2014Hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya OMS, ta sanar a wannan Juma'a (11.07.2014) cewa, an kafa wata cibiyar yaki da cutar Ebola ta kasa da kasa, a Conakry babban birnin kasar Guinea. Wannan cibiya za ta mayar da hankali ne, tare da tafiyar da tsarin duk wani kokarin da kasashen duniya ke yi, kan yaki da wannan cuta a kasashen yammacin Afirka, a cewar sanarwar da hukumar ta lafiya ta fitar domin bayyana wannan mataki da ta dauka.
Duk da cewa wannan cibiya za ta duba, ta kuma tsara ayyukan hukumomin kasar ta Guinea, tare da sauran kungiyoyin kasa da kasa kan wannan batu na Ebola, hukumar ta lafiya ta OMS, ba ta hana zirga-zirgar al'umma tsakanin kasashen da suka dade suna fama da wannan cuta ba, kasashen da suka hada da Guinea, Liberiya, da Saliyo.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe