Hadin kan Chaina da kasashen Larabawa
December 9, 2022Shugaba Xi Jinping na Chaina ya sanar da shirin kasar na kulla wata sabuwar dangantaka ta cinikayya da kasashen Larabawa, ya ce, a shirye kasar ta ke ta soma cinikin makamashi da kuma kudin Yuan na kasar, Shugaba Xi ya fadi hakan ne a yayin da ya halarci taron koli na kasashen Larabawa da ya gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiya. A na shi bangaren Mohammed bin Salman mai masaukin baki, ya yaba da ziyarar da kuma tayin karfafa dangantaka a cinikayyar man fetur da gas da Beijing.
Manarzarta na ganin yin hakan, wata dabara ce ta juya wa Amirka baya, musanman a yanzu da wasu daga cikin kasashen yamma, musanman Amirka, ke sukar Chaina a sakamakon yadda ta ki cewa uffan kan mamayar Rasha a Ukraine, baya ga haka, akwai barazanar da dalar Amirka ke fuskanta daga wannan huldar a tsakanin Chaina da kasashen Larabawa.