1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar dokar ritaya a Spain

January 29, 2011

Majalisar dokokin ƙasar Spain ta ƙara shekarun zuwa ritaya daga 65 zuwa 67 a matsayin wani ɓangare na matakan tsuƙe bakin aljihun gwamnati.

Wani tsoho mai ritaya da ke barcin rana a wani lambu a tsibirin CanaryHoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Spain majalisar dokoki ta sa hannu akan dokar ƙara shekarun yin ritaya daga 65 zuwa 67 a matsayin wani ɓangare na matakan tsuƙe bakin aljihu da gwamnati ke ɗauka domin rage basukan da ake bin ƙasar. An zartar da wannan dokar ne sa'o'i ƙalilan bayan da aka ba da sanarwar ƙaruwar yawan marasa aikin yi a ƙasar ta Spain. Sama da kashi 20 daga cikin ɗari na al'umar ƙasar suka rasa guraben aikinsu a watanni ukun ƙarshe na shekarar da ta gabata-inda hakan ke zaman matsayin rashin aikin yi irinsa mafi muni cikin shekaru 13 da suka gabata kuma mafi tsananta a nahiyar Turai. Hukumar zartarwar Ƙungiyar Tarayyar Turai na sa rai cewa ƙasar Spain ba za ta samu ci gaban tattalin arziƙi da zai kai ga rage yawan marasa aikin yi ba a wannan shekara.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal