1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar fasahar tace Zuma a Kano

November 2, 2016

Wani matashi mai suna Sani Ayuba Makama ya bullo da wata na’urar sarrafawa gami da tace zuman da ka iya kankankan da Kowacce tacecciyar zuma a duniya

Honig
Hoto: Fotolia/Jag_cz

Tun bayan da gwamnatin Njeriya ta bayyana cewar yanzu lokaci ya yi da ya kamata ace kungiyoyi da daidaikun mutane sun bada himma wajen shiga harkokin noma da kiwo a sakamkon faduwar farashin mai a kasuwar duniya, wannan kuma matakin a gefe guda ya sanya matasa tashi tsaye domin yin abubuwan da zai fishesu. A yanzu haka wani matashi mai suna Sani Ayuba Makama daya fito daga wani kauye a cikin jihar Kano a Najeriya ya kirkiro da wata na'urar tace zuma,to sai dai ba wai kawai injin tace zuma ya samar ba akwai ma Karin wasu a cewar sa.

Matashin yace koda yake na'urar ta dauke su tsawon lokaci kafin su samar da ita domin sai da suka yi nazari kuma suka jajirce tare da kwashe shekaru biyar kafin su samar da ita, a yayin da a hannu daya ta fara shiga hannun al'ummar gari.

Sau tari dai masu fasaha da kan kawo wani abu sabo ta hanyar yin wani nazari kan amfanar da jama'a  wajen samun abubuwan da suka kirkiro kana kuma su samarwa wasu guraben ayyuka ta hanyar koya musu irin baiwar da Allah ya huwace musu,Sani Usman daya ne daga cikin yaran dake karbar horo daga gun matashin daya kirkiro da na'urar tace zuman.

Harkokin Zuma dai na zama wani bakon abu a mafi yawancin kasashen Afirka amma yanzu haka manoman sun bazama domin karo ilimin habaka harkokin Zuman a zamanan ce, a inda matasa irin su Sani Ayuba suka fara baze kolin baiwar da Allah ya basu ta kirkiro da na'aurar tace zuman domin tallafawa jama'a.