Sabuwar gwamnati a Irak
November 25, 2010A yau ne aka rantsar da Frime Minista mai ci Nuri al Maliki a matsayin Frime Ministan ƙasar Irak a hukunce, a ka kuma gayyace shi ya kafa sabuwar gwamnati . Wannan gayyata da Maliki ya samu daga shugaban ƙasa Jalal Talabani, ta zo ne sakamakon wata yarjejeniya da su ka ƙulla domin waraware rikicin wanda ya ci zaɓe, a zaɓukan ƙasar da aka gudanar a watan Maris da ya gabata, wanda kuma aka ɗauki tsawon watanni takwas ana yi.
A yanzu haka dai an bayyana wa ɓangarorin siyasar ƙasar, yadda za su gudanar da yarjejeniyar samun ministoci a sabuwar gwamnatin da za'a girka.
Banda Maliki, da ya hito daga ɗarikar Shi'a, da shugaban ƙasa Talabani wanda baƙurde ne, yarjejeniyar ta ambaci wani balarabe ɗan sunni, a matsayin kakakin majalisar dokokin ƙasar.
Tsohon Firayima Ministan ƙasar, Iyad Allawi zai jagoranci hukumar kula da tsaro.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Umaru Aliyu