1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaHaiti

An rantsar da sabuwar gwamnatin wucin gadin Haiti

Suleiman Babayo LMJ
April 25, 2024

Sabon Firaminista Patrick Boisvert ya dauki madafun ikon gwamnatin wucin gadin kasar Haiti inda yake da jan aikin tabbatar da tsaro gami da tsara zabuka a kasar mai fama da tashe-tashen hankula.

Haiti mai fama da tashe-tahsen hankula
Haiti mai fama da tashe-tahsen hankulaHoto: Odelyn Joseph/AP Photo/picture alliance

An rantsar da sabuwar gwamnatin wucin gadin kasar Haiti karkashin sabon Firaminista Patrick Boisvert wanda ya kasance ministan kudi a gwamnatin da ta shude, ta tsohon Firaminista Ariel Henry wanda ya ajiye aiki a hukunmance abin da ya share hanyar kafa sabuwar gwamnati a wannan kasa mai fama da tashe-tashen hankula.

Sabuwar gwamnati ta kumshi wakilai daga jam'iyyun siyasa na kasar da kungiyoyin fararen hula gami da shugabannin addini.

Gwamnatin wucin gadin ta Haiti tana da jan aikin tabbatar da zaman lafiya da tsara zabuka a kasar, wadda ta yi kaurin suna na kungoyoyin 'yan daba.