Sabuwar gwamnatin Kenya na neman wargajewa
December 8, 2005Kimanin saoi 12 bayan sanarda sunayen ministoci da suka maye gurbin tsoffin ministoci 30 da shugaba Kibaki ya kora a watan da ya gabata,sai kuma ga shi a yau sabbin ministocin akalla 2 daga cikinsu da kuma mataimakansu 15 sun sanarda cewa ba zasu karbi wadannan mukamai ba.
Yawancinsu sunce Kibaki bai tuntube su ba kafin sanarda sunayen nasu a jiya laraba,sunayen da tuni da yawa sukayi korafin cewa,yan hannun daman Kibaki ne da kuma abokansa na kut da kut.
A ranar 21 ga watan nuwamba ne kuriar jin raayin jamaa da aka gudanar, taki amincewa da batun sake tsara kundin mulkin kasar wanda Kibaki ya nema da ayi.
An gudanar da kuriar ce bayan kanfe da ya kawo rarrabuwar kawunan tsoffin ministocin,tare da haddasa mummunan rikici da ake ganin zai bazu cikin kasar wadda ada ake ganin itace tudun mun tsira a yankin gabashin Afrika.
Wadanda Kibakin ya zaba a matsayin ministan kula da harkokin kananan hukumomi da kuma na muhallai Musikari Kombo da Orwa Ojedeh,sun baiyana cewa,ba zasu karbi wadanan mukamai ba saboda Kibaki bai tuntube su ba hakazalika,zaben ministocin wani cin mutunci ne ga yan kasar ta Kenya.
Shi dai kombo shine shugaban jamiyar FORD-Kenya wadda take bangare ne ta gwamnatin gamin gambiza dake mulkin kasar,har zuwa lokacinda ta balle daga uwar jamiyar game da batun sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Ojedeh,babban abokin Raila Odinga,tsohon ministan kula da hanyoyi na kasar wanda kuma ya jagoranci adawa da sabon kundin,yace bai ji dadai ba cewa wasu daga cikin yan jamiyarsa ta LDP sun karbi wadannan mukamai,duk da cewa an sauke abokansu da dama.
Da farko dai ana ganin cewa nada sabbin ministocin da Kibaki yayi,zai kawo karshen kiki kaka na siyasa da kasar ta shiga makonni biyowa bayan kin amincewa da batun sake kundin tsarin mulkin kasar da kusan kashi 60 cikin dari na jamaar kasar sukayi, cikin kuriar raba gardama ta farko da aka taba gudanarwa a kasar.
Masu lura da alamura da dama sun sa ran cewa,shugaban Kenyan wanda bayan amincewa da sakamakon kuriar, ya kuma sauke dukkan ministocinsa,karo na farko a tarihin kasar,zai sanarda kafa gwamnatin hadin gwiwa da zata hada da abokan hamaiyarsa da kuma magoya bayansa.
A maimakon haka,Kibaki ya sauke Odinga da wasu 6 yan jamiyar LDP wadanda suka baiyana adawarsu game da sobon daftarin wadda ake ganin zai mika dukkan iko ga shugaban kasa kadai.
Jaridun kasar Kenya da masu lura da alamuran siyasa na kasar,sun soki lamirin shugaba Kibaki,suna masu zarginsa da kin bin kiraye kiraye da jamaa sukeyi na kawo sauyi, sakamakon sako sako da yake yi da mulki tun nada shi 2002 tare da taimakon jamiyar LDP.
Sun ci gaba da cewa,zaben ministocin da Kibaki yayi ya nuna a fili cewa,shugaban na Kenya bai san abinda da yawa na jamaar kasarsa miliyan 32 suke bukata ba,musamman wajen samarda aikin yi,da kawo karshen kabilanci da inganta tattlin arzikin kasar.