Sabuwar hulda tsakanin Amirka da Cuba
July 20, 2015Kasashen Amirka da Cuba sun sake maido da huldar diplomasiyarsu bayan shekaru 54 na zaman doya da manja a tsakaninsu. Kasashen biyu sun tabbatar da hakan a ranar Litanin din nan inda suka gudanar da wani biki a birnin Washington wanda ya samu halartar ministan harakokin wajen kasar ta Cuba Bruno Rodriguez da kuma mataimakin sakataren harakokin wajen kasar Amirkan Roberta Jacobson wadanda suka jagoranci tawagogin kasashen biyu a gurin wannan biki wanda ya samu halartar sama da mutune 500.
Tuni dai aka sanya tutar kasar ta Cuba a ofishin jakadancin kasar ta Cuba a birnin Washington.Sai dai sai a watan gobena Agusta ne za a hauda tutar kasar Amirka din a ofishin jadancin kasar a birnin Havana lokacin ziyarar da sakataren harkokin wajen kasar Amirkan John Kerry zai kai a kasar ta Cuba.