1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar kungiyar 'yan tawaye a Kwango

Zulaiha Abubakar
February 22, 2018

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar za a iya fuskantar wahalar samar da kayan agaji a a yankin Tanganyika na Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.

Militär Kongo
Sojojin Kwango na fafatawa da 'yan tawayeHoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/D. Honl

 

A yayin da tashe-tashen hankula ke dada kamari a yankin Tanganyika da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar da wani gargadin gyara kayan ka bisa hangen abin da ta ce ka iya faruwa sakamakon rashin isar kayan agaji ga wadanda rikici a kasar ya rutsa da su. Hukumar ta kara da cewar yankuna da dama a yankin suna ganin masifa ba kadan  ba wacce ke sanadiyyar raba jama'a da muhallansu. Akwai dai wutar  rikicin kabilanci tsakanin kabilar Twa da  Luba da kuma sauran kabilu wacce ke dada ruruwa a dai-dai lokacin da mummunan tashin hankalin da yake faruwa tsakanin sojojin kasar da wasu 'yan tawaye wanda aka fara tun a watan Janairun wannan shekara ya dauki wani sabon salo sakamakon dada samun bayyanar wasu sababbin kungiyoyin, wadanda suke barazanar kassara yankin gaba daya. Rahotanni sun yi nuni da cewar dubban jama'ar da suka tsere daga yankin zuwa garin Kalemie don tsira da rayukansu sun bayyana labarai masu firgitarwa da suka hada da kai hare-hare a kauyukansu da yi wa mutane yankan rago da sace mutane da kuma cin zarafin mata, inda hukumar ta ce tana da rahoton da ya nunar da cewa sama da mutane 800 aka yi wa kisan gilla, baya ga wadanda aka sace da wadanda aka ganawa azaba a makwanni biyu na farko na wannan wata na Fabrairu da muke ciki kawai.

Halin da 'yan gudun hijira ke ciki a KwangoHoto: Reuters/M. Nichols

 

Halin kunci bayan gudun hijira

 

A cikin shekara ta 2017 da ta gabata dai wasu takwarorin aikin Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya sun fitar da rahotanni sama da dubu 12 na cin zarafin dan Adam a Tanganyika da kuma makwabtan garuruwa kamar Pweto zuwa sauran gurare da rikicin ya ke dada fantsama. Hukumar ta kara da cewar a kwai yi wu war karuwar yawan adadin mutanen da rikicin ya shafa tun da ba za a iya kai wa ga wasu wuraren ba sakamakon hatsarin da yake tatttare da hakan. Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango dai ta jima tana fama da rikice-rikice, kama daga na kabilanci da 'yan tawaye da kuma na siyasa.