Sabuwar mai gabatar da karar Kotun ICC
June 15, 2012An rantsar da matar nan 'yar asalin kasar Gambiya Fatou Bensouda a matsayin wadda ta maye gurbin Luis Moreno-Ocampo dan kasar Argentina tsohon mai gabatar da kara na kotun hukunta mayan laifufuka ta ICC a yau juma'a.
Matar dai 'yar shekaru 51 a duniya ta kasance mataimakiyar babban mai gabatar da kara a kotun tun a shekara ta 2004.
A can farko ta taba rike mukamin ministan harakokin shari'a na gambiya kamun daga bisani ta yi iaki a kotun kasa da kasa ta Rwanda wato (TPIR) da ke da cibiyarsa a birnin Arusha na Tanzaniya.
Yanzu haka dai madam Fatou Bensouda nada jan aiki a gabnta inda kotun ke shari'ar manyan laifufuka guda 7 akasarinsui a Afrika da suka hada da Cote d'Ivoire,Jamhuriyar Demokradiyar Kongo da kuma Libiya.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Zainab Mohammed Abubakar