1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar majalisar dokikin ƙasar Masar ta soma zaman taron ta na farko

November 22, 2011

Rubuta kudin tsarin mulki da kuma wasu dokokin wannan shi ne aikin da sabuwar majalisar dokokin da aka ƙaddamar za ta mayar da hankali a kai

Fouad Mebazaa,shugaban gwamnatin wucin gadi na ƙasar TunisiyaHoto: AP

Sabuwar majalisar dokoki da aka girka a ƙasar Tunisiya bayan faɗuwar gwamnatin Zine Abdnie Ben Ali ta soma zaman taron ta na farko a birnin Tunis.yan' majalisun guda 217 da aka zaɓa daga jam'iyyun siyasa daban daban a cikin watan oktoban da ya gabata su ne ke da alhaki rubuta kudin tsarin mulki na ƙasar.Shugaban gwamnatin wucin gadin Fouad Mebazaa, shi ne ya jagorancin bikin ƙaddamar da sabuwar majalisar dokokin;

wanda dabra da taron wasu ɗarruruwan jama'ar galibi magoya bayan ƙungiyoyin kare hakin bil adama da na fara fula; suka gudanar da zanga zanga domin ƙara jan hankali sabin hukumomin da cewa su yi taka tsantsan da buƙatun yan ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar