Sabuwar majalisar ministoci a kasar Guinea
January 5, 2016Talla
Sabuwar Ministar kula da tattalin arzikin kasar Malado Kaba 'yar shekaru 44 da haihuwa, ta kwashe mafi yawan lokutan ayyukanta a sashen kula da cigaban kasashe na kwamitin Tarayyar Turai, yayin da takwararta ta harkokin waje Makale Kamara, ita kuma ta taba rike mukamin ministar harkokin noma a lokacin mulkin soja na Lansana Conte daga shekarar 1984 zuwa 2008 kuma ta kasance jakadiyar kasar ta Guinea a Faransa da Senegal.
Sai dai duk da arzikin karkashin kasa da Guinea ke da shi, mafi yawan 'yan kasar na cikin mawuyacin halin talauci a wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya.