1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamhuriyar Nijar: Sabuwar makarantar diflomasiyya

Salissou Boukari SB
January 26, 2026

A Jamhuriyar Nijar, gwamnatin kasar ce ta kafa wata sabuwar cibiyar horas da jami’an Diflomasiyya wacce ake kira "National Institute of Diplomatic and Strategic Studies" domin karfafa hulda da kasashen tere.

Janar Abdourahamane Tiani shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar
Janar Abdourahamane Tiani shugaban mulkin sojan Jamhuriyar NijarHoto: Boureima Hama/AFP

A Jamhuriyar Nijar, gwamnatin kasar ce ta kafa wata sabuwar cibiyar horas da jami’an Diflomasiyya wacce ake kira "National Institute of Diplomatic and Strategic Studies". Inda ta ce samar da wannan cibiya ta horo ta INEDS, zai taimaka wajen cike gibin da ake da shi na rashin makaranta irin wannan ta kasa ta horas da jami’an diflomasiyya da kuma kara sani ga sauran jami'an ofishin jakadanci. Koma da yake yayin da wasu ke yaba matakin, wasu kuma na ganin ba wannan ne ke a gaban ‘yan kasar ta Nijar ba.

Tasirin makarantar

Shi dai kirkira wannan sabuwar cibiya ta INEDS, na da nufin samar da cikeken horo na kwarewa ga sabbin ma'aikata da aka dauka a cikin ma’aikatu na diflomasiyya da kuma kara sani na a fannin na difflomasiyya ga jami'an diflomasiyya da tuni suke aiki a ma’aikatu daban-daban na kasa da ma wakilcin kasar ta Nijar a waje.

Janar Abdourahamane Tiani shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar a wajen taroHoto: AFP

Hakan yana nufin horar da ma'aikata daga wasu ma’aikatu na gwamnati ko masu zaman kansu da ke aiki a cikin yanayi na kasa da kasa. Seidik Abba, dan jarida ne kuma masanin siyasar kasa da kasa da tafiya ta difflomasiyya ta duniya ya yi tsokaci kan wannan sabuwar cibiya wanda ya ce za ta taimaka wajen daukaka difflomasiyyar kasar.

Kaman yadda aka sani a cewar masana, shi dai aikin diflomasiyya, aiki ne na dan aike na kasa da zai je wata kasa ko wani waje ya yi magana da yawun wanda ya aika shi, wanda ake ganin kuma yin hakan na da bukatar kwarewa a fannin iya magana da hakuri, wanda a cewar Kassoum Issa, Malamin makaranta mai ritaya, kuma tsohon jagoran babbar kungiyar malaman makaranta ta kasar Nijar, bikin magaji ba zai hana na magajiya ba domin kuwa shi ilimi wajibi ne a neme shi a ko’ina.

Burin da aka saka a gaba

Ga burin dai da aka sa wa gaba ga wannan cibiya ta horo ta INEDS shi ne na ganin ta zamana wata babbar cibiyar bincike, da nazarin dabaru, da hangen nesa, inda za a gudanar da bincike kan manyan batutuwan da suka shafi yankin ko ma na kasa da kasa, wanda ake ganin babbar dama ce har ma ga kasashe aminnai da kuma makwaftan kasar ta Nijar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani