1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar rayuwa bayan rikicin zabe a Cote d'Ivoire

June 20, 2019

Shekaru biyu da suka gabata 'yan gudun hijirar sun soma dawowa gidajensu domin buda sabon babi na rayuwa inda harkoki suka fara kankama a garin  Tabou dake da nisan kilometa 400 daga Abidjan babban birnin kasar

Afrika Fischerei l Mitarbeiterinnen in der Côte d'Ivoire
Hoto: USCOFEP Côte d'Ivoire

A cikin yanayi na raha yara a kauyen Ranuike dake a nisan kilo mita daya daga Liberiya suka tarbi tawagar kungiyoyin agaji ta kasa da kasa dake kawo tallafi a wani mataki na farfado da rayuwar al'ummomin kauyen. Kungiyoyin agajin na koyawa matan kauyen sana'oin hannu don basu damar yin dogaro da kansu ta hanyar wani tsari mai lakabin AGR, lamarin da a cewar Mariette daya daga cikin matan kauyen yana taimaka masu matuka.

''Idan muka yi aiki na tsawon watanni biyu muna samun tallafin kundi CFA 30.000 Hakan na rufa mana asiri. Ta haka muke fadi ka tashi kuma yana taimakamana''

Hoto: picture-alliance/dpa

Kimanin euro miliyon biyu Jamus ta bayar domin samar da kyakkyawar makoma ga 'yan gudun hijrar Cote d Ivoire dake dawowa daga Liberiya ta hanyar koyar da su ayyuka domin tsayuwa da kafafunsu. A yayin wata ziyara da JakadanJamus a Cote d'Ivoire Michael Grau ya kai wata cibiya da ake koyar da mata aikin hannu kamar sabulu dake kauyen Ranuike, ya karfafa batun sake farfado da tattalin arzikin yanki a matsayin hanya mafi cancanta ta samarwa al'ummomin kyakkyawar rayuwa.

''Aikin samar da kudaden shiga na daya daga cikin wannan tsari, kuma abin na ban shawa yadda matan kauyen ke bayar da himma. Daya daga cikin galabar da aka samu shine yadda kudaden da aka tara ya bayar damar sayen injin markade''

Sai dai kasancewar watanni kalilan suka rage a gudanar da zaben shugaban kasa na 2020 a kasar ta CIV, wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da suka fuskanci ukubar tashin hankali a 2010 na fargabar sake komawa gidan jiya.