1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar shugabar riko a Afirka ta Tsakiya

January 20, 2014

A tsakiyar rikicin da take fama da shi, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta samu sabuwar shugabar rikon kwarya wato Catherine Samba-Panza.

Zentralafrikanische Republik Catherine Samba-Panza wird Übergangspräsidentin
Hoto: Reuters

A zaman da suka yi a Bangui babban birnin kasar, wakilan majalisar wucin gadin kasar sun zabi shugabar hukumar gudanarwar birnin Bangui, Catherine Samba-Panza a matsayin shugabar rikon kwarya. Hakan dai ya zo ne daidai lokacin da kungiyar EU a Brussels ta amince ta taimaka wa dakarun Faransa da na Afirka da ke wannan kasa mai fama da tashe-tashen hankula.

Catherine Samba-Panza ta yi nasara ne a zagaye na biyu na zaben da yawan kuri'u 75 a kan Desire Kolingba dake zama dan tsohon shugaban kasa marigayi Andre Kolingba, wanda ya samu kuri'u 53. Zaben dai ya gudana ba tare da wata matsala ba. Ita dai shugabar hukumar gudanarwar birnin Bangui wato Samba-Panza ita ce mace ta farko da ta taba samun wannan mukami a kasar.

Catherine Samba-PanzaHoto: Reuters

A jawabin da ta yi bayan an zabe ta, Samba-Panza ta nuna farin cikin da wannan nauyin da aka dora mata.

Shugaba ta kowa da kowa

"Abin sosa rai ne da kuka nuna amincewarku da ni har kuka zabe ni zuwa wannan mukami na shugabar wucin gadi, kuka kuma dora mun alhakin jagorantar wannan kasa da ma shirya zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki tare da maido da kundin tsarin mulkin wannan kasa ta mu ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A dalilin haka, ni zan kasance shugaba ce ta kowa da kowa. Shi ya sa ina kira ga dukkan 'yan kasa da su bani haɗin kai dan mu ga bayan wannan rikicin."

Yanzu dai Samba-Panza ta maye gurbin tsohon jagoran 'yan tawaye kuma shugaban wucin gadi, Michel Djotodia wanda ya yi murabus a ranar 10 ga watannan na Janeru sakamakon matsin lamba daga kasashen Afirka.

Tallafi daga tarayyar Turai

Wannan zaben ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar tarayyar Turai ta yanke kudurin tura sojoji kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bayan wani taron ministocin harkokin wajen kungiyar a birnin Brussels. Kawo yanzu dai Faransa ce kadai ta girke sojojinta a kasar, sai dai sojojin da yawansu ya kai 1600 ba za su iya yin wani abin kirki na kwantar da kurar rikicin kasar ba.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter SteinmeierHoto: DW/B. Riegert

Jamus ma ta ce za ta ba da gudunmawa amma ba ta sojoji ba. In ban da jiragen saman jigilar sojoji da kaya da kuma man jirgin sama, Jamus ba za ta iya ba da karin taimako ba, inji ministan harkokin wajenta Frank-Walter Steinmeier.

"Mun taimaka a Mali, inda aka kwantar da kurar rikicin amma ba a warware matsalar ta ba. A saboda haka daga bangaren Jamus, ina ganin za mu fi iya taimakawa a can fiye da a Janhuriyar Afirka ta Tsakiya."

Kalubale a gaban sabuwar shugabar

Shin ko sabuwar shugabar za ta iya magance rikicin tsakanin Kiristoci da Musulmi wanda aka kwashe watanni 13 ana yi. Paul Simon Handy mai sharhi ne a cibiyar nazarin harkokin tsaro ta ISS dake birnin Pretoria na Afirka ta Kudu.

"Zai yi wuya kwarai amma abu ne da za a iya yi. Ko da yake an kwashe watanni ana tashe-tashen hankula, amma ba su kai mizanin da ba za a iya magance su ba. Za ta zama shugabar da za ta yi sulhu, to sai dai za a dauki lokaci mai tsawo kafin a kai gaci."


A cikin wata sanarwa shugaban Faransa Francois Hollande ya ce yanzu ya rage wa sabuwar shugabar ta cimma wani sulhu tare da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake matukar bukata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani