1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar zanga zanga a ƙasar Masar

July 8, 2011

Al'umma ta dage sai an ƙaddamar da cikkaken sauyi tare da hukumta waɗanda suka aikata kisan gila akan fara fula

Masu zanga zanga a MasarHoto: dapd

Duban jama'a a ƙasar Masar sun gudanar da zanga zanga domin samun ƙarin sauyi watannin shidda bayan faduwar gwamnatin Hosni Moubarak.mutanen waɗanda suka yi dandazo a dandali Tahrir dake ɗauke da ƙwalayen, da a jikinsu ke da rubuce rubuce irin cewa zamu ci gaba da yin juyin juya hali suna yin ƙorafin cewa basu ga canji ba har yanzu.

Wata yar jarida daga birni Alƙahira ta shaidda cewa masu yin boren da gaske suke yi ko a wannan karo. A sauran garuruwan na Alexandriya birnin na biyu mafi girma na ƙasar da kuma yanki arewa maso gabashi an gudanar da boren.Jam'ian tsaro sun ƙarawace wa zanga zangar kamar yadda suka yi alƙawari sai dai

kuma wasu rahotanin na cewa a yanki Suez an sha artabu tsakanin yan' sanda da masu yin zanga zangar.Masu yin boren dai na son a hukumta mayan sojoji da ke da hannu a cikin kisan jama'ar ƙasar a lokacin waccan zanga zanga.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu