1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Sadiq Khan ya sake lashe zaben magajin birnin London

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 4, 2024

Sadiq Khan mai shekaru 53, shi ne musulmi na farko da ya taba zama magajin garin birnin London, lokacin da aka fara zabarsa a shekarar 2016

Hoto: Peter Nicholls/Getty Images

Magajin garin birnin London na jam'iyyar Labour Sadiq Khan, ya sake lashe zaben Asabar din nan, kuma ya kafa tarihin cin zabe karo na uku a jere, bayan da ya doke Susan Hall ta Conservative.

karin bayani:Zaben magajin garin birnin London na kasar Burtaniya

Sadiq Khan mai shekaru 53, shi ne musulmi na farko da ya taba zama magajin garin birnin London, lokacin da aka fara zabarsa a shekarar 2016.

karin bayani:An kori shugaban jam'iyyar Conservative ta Britaniya

Sakamakon zaben dai ya nuna yadda firaministan Burtaniya Rishi Sunak da jam'iyyarsa ta Conservative ke ci gaba da fuskantar koma-baya a sha'anin siyasar kasar.