1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunwa ta karu saboda ta'addanci a Sahel

Martina Schwikowski USU/LMJ
October 21, 2020

Bukatar agajin gaggawa a kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar na karuwa. Ta'addanci da annobar COVID-19, sun sa yanayin ya kara tabarbarewa.

Mauretanien Beduinen an Brunnen
Sauyin yanayi da ke janyo fari da ta'addanci na janyo barazanar yunwa a yankin SahelHoto: Getty Images/AFP/A. Senna

An dai gudanar da taron neman agajin gaggawa ga kasashen yankin na Sahel da suka hadar da Nijar da Mali da Burkina Faso. An dai bayyana cewa wadannan kasashen ka iya fuskantar bala'in yunwa. Taron wanda ya gudana a birnin Kopenhagen na kasar Denmak, bayan kammala shi sun sanar da kudirin bayar da tallafin Euro miliyan 43 domin fara taimaka wa kasashen.

Karin Bayani: Jinkiri wajen kafa rundunar G5 Sahel

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi yekuwar bukatar samar da dalar Amirka biliyan daya domin bayar da agajin gaggawa a yankin na Sahel. Wannan ne ma ya sanya gudanar da taron wanda aka yi a karkashin hadin gwiwar Jamus da kungiyar Tarayyar Turai  EU, inda aka bayyanan cewa tilas a gaggauta samar da mafita ga kasashen na Mali da Nijar da Burkina Faso, domin tsamo su daga fadawa cikin bala'in karancin cimaka.

Al'ummomi da dama na bukatar agajin gaggawa a yankin SahelHoto: Andy Hall/Oxfam

Tallafin da aka bayar dai an kasa shi ne bisa yawan matsalolin, inda wakilin Tarayyar Turai yayin taron ya bayyana cewa an ware Euro miliyan 23 domin gudanar da ayyukan jin kai a kasashen, yayin da kuma za a yi amfani da Euro miliyan 20 wajen yaki da yunwa. 

Karin Bayani: EU na yaƙi da ta'addanci a Sahel

Yake-yaken kungiyoyi ta'dadda da sauran masu dauke da makamai, ya yi matukar bazuwa a yankin  Sahel cikin shekarun baya-bayan nan, inda kasashen NIjar da Mali da Burkina suke kan gaba wajen samun bazuwar kungiyoyin 'yan ta'adda. Haka kuma a kasashe kamar Nijar, wasu yankunan na fama da matsalar Boko Haram. Baya ga karancin abinci da yankin ke fuskanta, a taron an bayyana kasashe uku a matsayin wadanda suka fi ko wacce kasa a yankin na Sahel fuskantar barazanar fadawa rigingimu, sakamakon sauyin yanayi da karuwar al'umma, inda yanzu aka sanar da cewa yara da dama ne ba sa samun damar zuwa makaranta.Wata kididdiga sun yi nunita nunar da cewa mutane sama da miliyan 13 ne ke bukatar agajin gaggawa a iyakokin kasashen na Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani