1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sahihiyar hanyar warware rikicin Siriya

September 15, 2012

Fafaroma Benidikt na 16 da shugaba Assad sun ce hana shigo da makamai a Siriya ne mafita ga rikicin kasar.

++++ Alternativer Ausschnitt +++ epa03398423 A handout photo made available by Syria's Arab News Agency SANA shows Syrian President Bashar Assad (C-R) meeting with the U.N.-Arab League envoy, Lakhdar Brahimi (C-L), in Damascus, Syria on 15 September 2012 for talks that focused on the 18-month-old crisis in the country. Brahimi_s meeting with Assad is the first since he has replaced the former UN Secretary General Kofi Annan. Brahimi, who is on a three-day visit to Syria, held a series of meetings in Damascus with Syrian officials and opposition leaders in order to shape a clear perspective for his future initiative to end the crisis. EPA/SANA / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Babban mai shiga tsakani a rikicin Siriya Lakhdar Brahimi, ya fadi a wannan Asabar, bayan ganawa tare da shugaba Bashar al-Assad na Siriya cewar tabarbarewar harkokin tsaro a kasar ta Siriya wata barazana ce ga duniya baki daya.

A nashi bangaren, kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya ya ruwaito shugaba Assad na shaidawa mai shiga tsakanin cewar, nasarar aikin daya ke gudanarwa ta dogara ne ga manyan kasashen da ke samar da makamai ga 'yan tawayen Siriya, tare da basu horo da kuma samar musu da kudaden gudanar da ayyukan su, inda yayi kira a gareshi daya nemi su dakatar da yin hakan.

Kalaman na shugaba Assad dai na zuwa ne bayan da Fafaroma Benidikt na 16 da ke fara ziyarar aiki a kasar Lebanon wadda ke makwabtaka da Siriyar ya kwatanta shigo da makaman da ake yi zuwa Siriya a matsayin babban zunubi, tare da yin kira ga dakatar da hakan.

Ita kuwa kungiyar kare hakkin jama'a ta kasar Siriya, wadda cibiyar ta ke birnin London na Birtaniya cewa ta yi kimanin mutane 160 ne suka mutu a wannan Jumma'ar kadai, sanadiyyar bata-kashin da aka yi a kasar ta Siriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman