1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sai an dama da kowa a rigakafin corona

September 5, 2020

Yayin da ake ganin alamun cimma rigakafin cutar corona a duniya, wani babban jami'i ya ce dole ne a dama da kowa muddin ana son samun mataki na bai daya.

43. UN-Menschenrechtsrat | Tijjani Muhammad-Bande
Hoto: picture-alliance/KEYSTONE/S. Di Nolfi

Shugaban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya, Tijjani Muhammad Bande, ya yi gargadi game da bukatar wadata dukkanin sassan duniya da allurar rigakafin cutar corona, ganin hadarin da ke akwai muddin aka ware wata kasar ba tare da ta sami kariya ba.

Yayin da duniya ke hangen alamun nasarar samun rigakafin cutar ta corona, Tijjani Muhammad Bande, ya ce dole ne a dama da kowa a harkar.

Ya fadi hakan ne a wata hirar da ya yi da kamfanin dillancin labaran Associated Press, duk da cewar bangarorin duniya da ke hada magungunan na cewa za su wadata ko'ina da maganin na rigakafi.

Ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin kasashe tare da tausaya wa juna a wannan halin da aka shiga.