Sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayi a Kenya
August 4, 2010A ƙasar Kenya ɗimbin mutanene suka fito domin kaɗa ƙuri'a, a zamen jinrayi domin yiwa kuddin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima. Sakamakon wucin gadi ya nuna cewa, mutane sun amince da sabon kundin tsarin mulkin. Inda kimanin miliyan uku suka yi na'am da sabon tsarin, yayinda kasa da miliyan biyu suka kada kuri'ar rashin yarda. Manufar yin haka dai itace na kaucewa akuwar irin tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen ƙasar na shekara ta 2007. A wancan lokacin dai mutane fiye da 1,300 suka mutu, a faɗan ƙabilancin da ya ɓarke, inda yan adawa suka yi zargin tabka muguɗin zaɓe. Shugaban ƙasar ta Kenya Mwai Kibaki yace "Ina rogon Alummoin ƙasar mu dasu fito domin kada ƙuri'a, kuma yakama ta suyi hakan cikin sanyi". Shi kuwa frayim ministan ƙasar Raila Odinga yacewa yayi "Babu kokwanto wadanda za su amice zasu yi rinjaye, kana ina da yaƙinin kashi 70 cikin ɗari na masu kaɗa ƙuri'a zasu amince da sabon kuddin tsarin mulkin ƙasar. idan dai aka amince da sabon tsarin to zai rage ƙarfin da shugaba Mwai Kibaki ke da shi.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita. Ahmadu Tijjani Lawal