Sakamakon bincike Amirka kan Siriya
August 30, 2013Amirka ta ce ta tabbatar gwamnatin Assad ce ke da hannu a wajen amfani da makamai masu guba a ƙasar wanda ya kashe sama da mutane dubu da ɗari hudu suka rasu, ciki har da kananan yara.Sakataren harkokin wajen Amirkan John Kerry ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi a wannan Jumma'ar inda ya ƙara da cewar Siriya ta fi kowacce ƙasa a yankin Gabas ta Tsakiya yawan makamai masu guba.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Amirkan ke shirin afkawa Siriyan da yaƙi, inda Mr. Kerry ya ce matakin da za su ɗauka kan ƙasar zai zama tamkar aike wa da sako ga ƙasashe irin su Iran da kuma ƙungiyoyi irin su Hezbollah, sai dai ya ce ba za su bari abinda ya faru a Iraki ya maimaita kansa ba.
A daura da wannan, jami'an Majalsiar Ɗinkin Duniya da suka gudanar da bincike kan zargin amfani da makamai masu guba a yaƙin Siriya sun ce sun kammala bincikensu. Mai magana da yawun Majalisar Ɗinkin Duniya Martin Nesirky ne ya shaida hakan a wannan Jumma'ar, inda ya ƙara da cewar jami'an za su bar Siriya domin komawa bakin aikinsu don yin nazari kan shaidun da suka tattara kafin daga bisani su fidda sakamakonsu.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane