Sakamakon binciken Kotun ICC game da rikicin Kenya
December 15, 2010Kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta manyan lefikan yaƙi, da ke birnin the Hague ta bayyana sunayen mutanen da ta ke tuhuma da hannu a cikin rigingimun da su ka ɓarke bayan zaɓen ƙasar Kenya a shekara 2008, wanda su ka yi sanadiyar mutuwar mutane1.200.
Babban mai shari´a na kotun ICC Luis Moreno Ocampo ya za na sunayen mutane shidda masu hannu a cikin ta´asar:
" Binciken da mu ka gudanar ya gano cewar, akwai wasu manyan jami´ai na jam´iyar Orange Demokratic Party, da su ka kitsa wata maƙarƙashiyar aikata kisan kiyasu, mun tantance sunayensu kuma za su gurfana gaban ƙuliyya."
Wannan mutane kuwa sun haɗa da ministan ilimi mai zurfi, da na makamashi da kuma babban Sakataren gwamnati Kirimi Muthaura.Sannan akwai ministan kuɗi da kuma tsofan shugaban rundunar ´yan sanda ta ƙasa Mohamed Hussein Ali, sai kuma daraktan wata redio mai zaman kanta.
Sai dai kotun ta ce babu cikkakar shaida game da shugaban ƙasa Mwai Kibaki da Firayim Ministan Raila Odinga.
Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Umaru Aliyu