1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Labarin Wasanni: Kamaru ta lashe WAFCON

Suleiman Babayo LMJ
August 17, 2026

Kamaru ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta mata ta nahiyar Afirka a karon farko, kana an yi wasannin sada zumunci na shirye-shiryen wasannin lig na kasashen Turai.

WAFCON | 2026 | Nasara | Kamaru | Malawi
'Yan matan Kamaru sun taka rawar gani a gasar WAFCON ta banaHoto: AP Photo/picture alliance

A karon farko kasar Kamaru ta dauki kofin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Mata ta Afirka WAFCON, bayan ta doke Malawi da ci 3 da nema. Wannan ne dai karo na farko da kasar Malawi ta kai wasan na karshe, kuma an samu sauyi daga Najeriya wadda ita ke lashe kofin duk tsawon tarihi. Sai dai a bana Najeriyar ta gaza zuwa wasan kusa da ka karshe, bayan lashe kofin har sau 10 a tarihinta. Karo na hudu ke nan Kamaru na kai wa wasan karshe na cin kofin mata na Afirka, kuma sau uku a baya duk Najeriya ce take samun galaba a kanta.

Najeriya ta gaza kare kambunta, bayan lashe kofin WAFCON sau 10Hoto: Mansa Ayoola/Shengolpixs/IMAGO

Shugaban Hukumar Kula da Wasan Kwallon Kafa ta Duniya Gianni Infantino tare da takwaransa na Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka Patrice Motsepe sun halarci wasan karshen, wanda Maroko ta dauki nauyi. Tun da farko a wasan neman samun gurbi na uku kasar Aljeriya ta doke mai masaukin baki Maroko, inda aka tashi wasan 1 da 1. Sai dai Aljeriya ta doke ta da ci uku da biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida, abin da ya bai wa Aljeriya nasarar zama ta uku a wannan gasa.

Jamal Musiala yayin da Ismael Saibari li ke taimaka masa bayan ya fadiHoto: Markus Ulmer/Ulmer/Teamfoto/IMAGO

A karshen makon da ya gabata kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Turai, sun yi wasannin sada zumunta gabanin fara kakar-wasannin lig-lig a kasashen na Turai. Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich mai rike da kanbun Bundesliga na Jamus ta doke RB Leipzig da ci 3 da 1, sai dai dan kungiyar ta Bayern Munich mai tasiri Jamal Musiala ya fadi lokacin da ake shirin kare wasan.  Borussia Dortmund ta tashi 2 da 2 a wasansu da AS Roma ta Italiya da ta karbi bakunci. Yayin wannan wasa, Borussia Dortmund ta gabatar da 'yan wasan da za su yi mata wasannin Bundesliga na shekara ta 2026 da 2027.

Dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid, Kylian Mbappé Hoto: Andrea Comas/AP/dpa/picture alliance

Kungiyar Real Madrid ta Spaniya ta yi tattaki zuwa Jamus, inda ta doke kungiya Schalke da ci 3 da nema a filin wasan Schalke. Wannan lamari ya kankare duk wata murna da kungiyar ta Schalke take yi ta sake komawa rukuni na daya na Bundesliga gabanin fara kakar bana, bayan dogon zama a rukuni na biyu na Bundesliga. Shahararrun 'yan wasan Real Madrin da suka hada da Kylian Mbappé da Dean Huijsen da Carlos Espi wanda ya yi canji, su ne suka jefa kwallayen uku a ragar Schalke 04.

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani