1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU NATO Libyen

March 21, 2011

Ministocin harakokin waje na ƙasashen EU da ƙasashe membobin NATO sun kasa cimma matsaya guda game da yaƙin Libiya

Hoto: dapd

Ministocin harakokin waje na ƙasashe membobin Ƙungiyar tsaro ta NATO, sun gudanar da zaman taro a birnin Brussels na ƙasar Beljiam da zumar laluben hanyoyin kawo ƙarshen rikicin Libiya.

Wannan taro da ake iya dangawata da gociya bayan mari, ya zo ne kwanaki biyu bayan da rundunar ƙasa da ƙasa ta ƙaddamar da yaƙi a Libiya, da zumar kawo ƙarshen abinda ƙasashen su ka danganta da kisan mummuƙe da dakarun shugaba Khaddafi ke wa fara hulla, wanda ba su ci kasuwa ba runfuna ke faɗa masu.

A lokacin da yayi jawabi a wannan taro ministan harakokin wajen Finland Alexander Stubb ya jaddada manufar wannan yaƙi da rundunar ƙasa da ƙasa ta ƙaddamar:

Shugabannin kungiyar kawancen tsaro ta NATOHoto: AP

Matakin da mu ka ɗauka cika umurnin Komitin Sulhu ne na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ya ƙuduri ƙasashe su ɗauki dukan matakan da su ka wajaba, domin kare al´umomin Libiya,Kuma ƙasashe daban-daban na duniya wanda su ka haɗa da na Turai, Amurika da Ƙungiyar ƙasashen Larabawa da ma Ƙungiyar Tarayya Afirka, duk sun bada haɗin kai ga wannan matakin.

Sai dai Jamus da ke matsayin jagora a tsakanin ƙasashen EU ta bayyana adawa da tura sojoji a Libiya.Duk da cewar sauran ƙasashen EU ba su fito fili su ka la´anci Jamus ba, amma da alamun ta ciki ne ta na ciki, kamar yadda alamu su ka nuna a cikin jawabin minisatan harakokin wajen Luxembourg Jean Asselborn:

An samu bambanci ra´ayi da ƙasar Jamus, to amma ni ban zo nan ba, domin zargin gwamnatin Jamus game da matakin da ta ɗauka.

Ministan harakokin Jamus Guido Westerwelle da ya halarci taron na Beljiam ya ƙara jaddada matsayin da ƙasarsa ta ɗauka:

Ministan harkokin wajen Jamus Guido WeterwelleHoto: dapd

Ina sane da cewar bai kamata ba a samu saɓanin ra´ayoyi tsakanin ƙasashen Ƙungiyar Tarayya Turai a game da batutuwa masu mahimmanci, to amma duk da haka, gwamnatin Jamus ya yanke shawara ƙin tura sojojin a cikin rundunar ƙawace zuwa Libiya sabodan dalilanta na ƙashin ƙanta.

Wannan yaƙi da ƙasashen Faransa, Birtaniya da Amurika su ka fara ƙaddamawra a Libiya ya jawo rabuwa kanu tsakanin Ƙungiyar Ƙasashen EU da ma na ƙungiyar tsaro ta NATO, wanda su kasa cimma matsaya guda game da ɗamkawa Ƙungiyar, jagorancin yaƙin.Faransa da a halin yanzu ta fi nuna zaƙewa a cikin batun, ta bayyana adawa da baiwa NATO wuƙa da nama a cigaban gwagwarmaya da shugaba Mohamar Ƙkadafi.A tunanin Fransa, idan Ƙungiyar tsaro ta NATO ta ɗauki jagorancin yaƙin za a samu masu adawa da shi daga ɓangaren ƙasashen larabawa ta la´akari da ƙwan jinin da NATO ta yi a wannan yanki.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala