1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron G20 a Landan

April 7, 2009

Ra´ayoyin jama´a a game da sakamakon taron Ƙungiyar G20

Taron G20 a LandanHoto: AP

A ranar Biyu ga watan Afrilun nan ne Shugabannin Manyan ƙasashen ashirin da suka ci gaba a fannin masana'antu na G20 suka gudanar da babban taron a birnin London don neman hanyoyin warware matsalar koma bayan tattalin arzikin da duniya ke fama da ita, inda kuma suka cimma matsaya akan batutuwa daban-daban, shirin ciniki da Masanaántu na wannan mako, zai duba sakamakon taron da kuma irin martanin da Jama'a suka mayar.

Prime Ministan Engla Gordon Brown a jawabin buɗe taron ya bayyana mahimmancinsa:Wannan ita ce ranar da ɗaukacin ƙasashen Duniya suka tattaru a wuri guda, domin shawo kan matsalar koma bayan tattalin arzikin da Duniya ke fama da ita, ba wai da yawun baki ba, a'a da wani ingantaccen tsari farfado da tattalin arziki da samar da sauye-sauye.

Kalaman Prime Ministan Birtaniya Gordon Brown kenan a wajen Taron Ƙungiyar ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arziki a duniya na G20.

Bayan tsawon lokacin da duniya ta ɗauka tana dakon wannan taron, kasancewar ko wace ƙasa na ɗanɗana raɗadin matsalar, wadda ta zama ruwan dare gama Duniya, Shugabannin ƙasashen na G20 sun hallara , inda kuma suka cimma daidaito akan batutuwa daban-daban.

Prime Ministan Birtaniya Gordon Brown, wanda shine mai masaukin baki, ya yi jawabi akan sakamakon Taron:

Munyi amannar cewar, idan ana bukatar ci gaba mai dorewa, to, kuwa tilas kowa ya taka rawar gani, harkar cinikayya ce zata kasance tubalin hakan. Tsohuwar yarjejeniyar da aka cimma a Washington a yanzu ta zama tarihi. A yau mun cimma wata sabuwar matsaya, na cewar zamu dauki mataki na bai daya, wajen tinkarar matsalolin da muke fuskanta, kuma zamu yi duk abin da ya wajaba domin farfado da bunƙasa da samar da ayyukan yi, kana mun kuduri anniyar sake tabbatar da yardar jama'a ga tsarin cibiyoyin tua'mmuli da kudaden mu, game da daukar matakan hana afkuwar irin wannan matsalar a nan gaba. Ba zamu ce za'a ga sakamako cikin gaggawa ba, amma idan muka bi alkawura shidan da muka dauka, to, kuwa zamu iya taƙaita matsalar, mu kuma ceto ayyukan yi.

Taron ya ware kuɗi Dala Tiriliyon Biyar domin shawo kan matsalar nan da shekara ta Dubu Biyu da Goma. Hukumomin kasa da kasa, wadanda ke harka da kudi zasu sami Dala Tiriliyon daya, inda A susun bayar da lamuni a Duniya IMF zai sami Dala Miliyan Dubu Ɗari Bakwai da Hamsin. Kaso na Dala Miliyan Dubu Ɗari Biyu da Hamsin ,kuwa, za'a sanya shine ga harkar Cinikayya, game da ɗaukar matakan kammala yarjejeniyar data shafi cinikayya a Duniya, wadda aka fi sani da ta Doha.Mr Brown ya ci gaba da cewar:

A karon farko ɗaukacin ƙasashen duniya, sun ɗauki matsayi na bai ɗaya, wajen tsabtace Bankuna, da farfado da bayar da rance. Muna yin namijin ƙoƙari wajen sake fasalin cibiyoyin kuɗinmu na ƙasa da ƙasa, saboda wannan lokaci da kuma nan gaba. Kuma mun jaddada ƙudurin mu na tallafawa ƙasashen da suka fi talauci a Duniya, mun ware wasu kuɗaɗe domin wannan lamarin, dama ingantacciyar hanyar farfado da tattalin arziki.

To, bayan Taron dai Shugabannin manyan ƙasashen sun nuna gamsuwar su ga matsayar da aka cimma. Shugaban Amurka, Barak Hussaini Obama, wanda a ƙasar sa ne matsalar ta kunno kai, yace a wurin sa dai Taro ya cimma nasara: Ko da wani mizani ka auna, Taron birnin London ya zama abin tinƙaho a tarihi, saboda girman ƙalubalen da muke fuskanta da kuma girma da yanayin da muka mayar da martani cikin gaggawa.

Shi kuwa Shugaban hukumar tarayyar Turai, Hose Manuel Barroso cewa yayi yanzu ba abinda ya saura sai aiki:Idan ka dubi abinda Taron ya cimma, zaka ga cewar an sami dimbin fata, fiye da wanda aka zata. A baya mun fadi abinda zamu yi a Taron, a yanzu kuma zamu yi abinda muka fada a Taron."

To gabannin fara Taron dai Ƙasashen Jamus da Faransa sun buƙaci samar da tsauraran ƙaidoji ga sha'anin kuɗi da yin watsi ga shirin kai ɗauki ga cibiyoyin dake tangal-tangal. Shugaba Nikolas Sarkorzy na Faransa ya ma furta cewar, idan kudirin da aka zartar bai cimma bukatun sa ba, to, kuwa zai fice daga zauren Taron. Sai dai kuma bai aiwatar da barazanar ba, maimakon haka ma cewa yayi:

Mataki na farkon da muka cimma, shine ƙara sanya ido akan hada-hadar kudaɗe tsakanin ƙasashen Duniya. Wannan buƙata ce mai karfi, wadda Faransa da Jamus ke da ita.

A nata ɓangaren, Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Mekel, tsokaci tayi akan daidaiton da aka samu:Mun sami fahimtar juna a game da tabbatar da haske a kasuwannin kuɗaɗe. Shugabannin ƙasashe dana Gwannatoci sun rattaba hannu akan wannan daftari. Sai dai zuwa gaba za'a ƙara bayani akan hanyoyin tabbatar da hakan.

Shi kuwa Abarshi Magalma, Mataimakin Magatakardan Kwamitin ƙwararrun dake bayar da shawara akan lamuran da suka shafi tattalin arziki a Jamhuriyar Nijar, cewa yayi akwai bukatar tabbatar da cewar Shugabannin kasashe masu tasowa su daina dogaro akan wasu hukumomi domin warware matsalolin su na cikin gida.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadissou Madobi