1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron NATO game da Libiya

June 8, 2011

Ministocin tsaro na ƙasashe membobin ƙungiyar NATO sun yanke shawara matsa ƙaimi wajen kai hare-hare a Libiya.

Hoto: picture alliance/dpa

Ministocin tsaro na ƙasashe membobin Ƙungiyar tsaro ta NATO sun jaddada kira ga shugaban ƙasar Libiya Mouammar Khaddafi ya yi murabus.

Ministocin sun yi wannan kira a wani zaman taron da su ka shirya wannan Laraba a birnin Brussels na ƙasar Beljiam.

To sai dai a wani jawabi da yayi jiya shugaba Khaddafi ya ce sai dai a kashe tsohuwa kan daddawarta.

A wannan Larabar jiragen yaƙi masu saukar angulu na ƙungiyar tsaro ta NATO sun kai sabin hare-haren a birnin Tripoli wanda shine hari mafi girma da ta kai tun bayan da ta kaddamar da yaki kan Libiya.

Sakatare Janar na NATO Anders Fogh Rasmussen ya ce za su cigaba da kai hare-haren har sai Khaddafi ya bada kai bori ya hau:Dukkan ministocin sun amince a cigaba da kai hare-hare ta sama har sai an cimma burin da aka sa gaba, saboda haka mun tsawaita wa´adin hare-haren har zuwa karshen watan Yuni.

A zaman taron na wannan Laraba NATO ta ce ba za ta kai hari ta ƙasa ba.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Halima Balaraba Abbas