1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron NATO game da Siriya

June 26, 2012

NATO ta ba da goyan baya ga Turkiyya amma ba ta yanke shawara ƙaddamar da yaƙi kan Siriya ba.

NATO Secretary General Anders Fogh Rasmussen briefs the media after a meeting of the North Atlantic Council at the Alliance headquarters in Brussels June 26, 2012. NATO member states condemned Syria on Tuesday for its shooting down of a Turkish military jet, calling it "unacceptable" and demanding that Damascus take steps to prevent further incidents. REUTERS/Francois Lenoir (BELGIUM - Tags: POLITICS MILITARY)
Jawabin Rasmussen game da SiriyaHoto: Reuters

Kungiyar tsaro ta NATO ta shirya wani zaman taron gaggawa a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam bisa buƙatar ƙasar Turkiyya.

Hukumomin Ankara sun buƙaci NATO ta yi zama na mussamman domin yin nazari game da batun kakkaɓo wani jirgin sama mallakar Turkiya da ƙasar Siriya ta yi a makon da ya gabata.

Bisa dokokin NATO, da zaran a ka kaiwa ɗaya, daga cikin ƙasashe 28 membobin ƙungiyar hari, tamkar kaiwa sauran hari ne.

A zaman taron, jikadodin ƙasashen NATO sun yi tur da Allah wadai da harbo jirginTurkiya, sai dai ba su ɗauki matakin kaiwa Siriya yaƙi ba, kamar yadda Sakatare Janar na NATO Anders Fogh Rasmussen ya bayyana:

Mun tattana wannan matsalar, baki ɗaya mun bada haɗin kai ga Turkiyya, ba mu tsaida shawara ƙaddamar da yaƙi ba ga Siriya, sai dai za mu ci gaba da bin al'amarin sau da ƙafa.

Cemma dai tun ɓarkewar rikicin Siriya fiye da shekara guda, ma'amala ta gurɓace tsakanin fadodin mulkin Ankara da Damascus.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Yahouza
Edita: Usman Shehu Usman