1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon wasannin Jamus da Turai da Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar MAB
October 4, 2021

Ko kun san wacce ta lashe gudun fanfalaki na mata na Landan? Kun san cewa Bayern Munich ta sha kaye a wasan karshen mako a gasar kwallon kafa ta Bundesliga? Ku bibiyi shirin Labarin Wasanni don jin karin bayani

Großbritannien London Mary Keitany
Hoto: Reuters/M. Childs

 'yar tseren kasar Kenya Joyciline Jepkosgei ta lashe gasar gudun fanfalaki na mata wato Marathon da aka gudanar a birnin Landan na kasar Birtaniya, yayin da  Sisay Lemma dan kasar Habasha ya lashe gasar a rukunin maza. Wannan dai shi ne karo na farko da aka dawo wannan gasa ka'in da na'in, tun bayan bullar annobar coronavirus da ta shafi harkokin rayuwar yau da kullum a duniya ciki kuwa har da bangaren wasanni. Jepkosgei ta kammala tseren cikin sa'o'i biyu da mintuna 17 da dakika 43, yayin da Degitu Azimeraw ta zo ta biyu bayan da ta kammala cikin sa'o'i biyu da mintuna 17 da dakika 58. A nasa bangaren Lemma da ya gaza samun nasara a gasar gudun fanfalakin yayin gasar guje-guje da tsalle-tsalle da aka gudanar a kasar Japan, a wannan karon ya kammala tseren cikin sa'o'i biyu da minutuna hudu da dakika daya. Vincent Kipchumba dan kasar Kenya ne ya zo na biyu a rukunin na maza, inda ya kammala nasa tseren cikin sa'o'i biyu da mintuna hudu da dakika 28

Bayern Munich ta dibi kashinta a hannun Frankfurt

. A gasar Bundesliga ta kasar Jamus a ranar Jumma'ar da ta gabata Cologne ta lallasa kungiyar Greuter Fürth da ci uku da daya, kana a ranar Asabar Hertha Berlin ta kwashi kashinta a hannun Freiburg da ci biyu da daya, kana Stuttgart ta lallasa Hoffenheim da ci uku da daya. Augsburg kuwa ta sha kashi a hannun Borussia Dortmund da ci biyu da daya, haka kuma RB Leipzig ta lallasa Bochum da ci uku da nema. Ita kuwa Borussia Mönchengladbach ta bi Wolfsburg har gida ta kuma lallasa ta da ci uku da daya.

Nagelsmann bai ji da dadi ba a hannun FrankfurtHoto: Sven Simon/imago images

A wasannin da aka fafata a ranar Lahadi kuwa, Union Berlin ta bi Mainz har gida ta kuma samu nasara da ci biyu da daya kana. Ita kuwa Bayern Munich ta sha kashi ita ma a gida a hannun Frankfurt da ci biyu da daya,  ita ma dai Leverkusen ta bi Arminia Bielefeld har gida ta kuma caskara ta da ci hudu da nema. Kungiyar ta Bayern Munich ce ke saman tebur da maki 16 yayin da Leverkussen ke biye mata a matsayi na biyu ita ma da maki 16, sai kuma Borussia Dortmund da Freiburg ke bi mata a matsayi na uku da na hudu dukansu da maki 15.


Ghana ta dawo da tsohon kocinta Rahevac

Hukumar kwallon kafar Ghana ta nada sabon kociHoto: imago/S. Spiegl

 Kasar Ghana ta dawo da tsohon mai horas da 'yan kungiyar kwallon kafarta ta kasa wato Black Star Milovan Rahevac duk da cece-kucen da ake kan wannan mataki da mahukuntan suka dauka. Shi dai Rahevac ya koma Ghanan ne, bayan da aka kori mai horas da 'yan wasan na Black Star sakamakon gaza katabus da kuma sauka kan jerin teburin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na duniya da kungiyar ta yi.