Sakamakon yaki da ta'addanci a Masar
March 1, 2015Rundunar sojan kasar ta Masar ta yi wannan aiki ne tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sandar kasar a watan da ya gabata na Febrairu a yankin Sinai, yankin da ke fuskantar hare-haren 'yan ta'adda babu kakautawa a kan jami'an tsaron kasar. Tun dai da Shugaban kasar mai ci yanzu Abdel Fattah Al-Sissi ya saukar da zababben Ssugaban na wancan lokaci Mohamed Morsi a watan Yulin 2013, jami'an tsaron Masar suka dukufa wajen abun da suka kira yaki da 'yan ta'adda a yankin arewacin kasar, inda 'yan kungiyoyin jihadi suke da karfi.
Rundunar sojan kasar ta Masar ta ce farmakin da ta kai a biranen Al-Arich, da Zoueid da kuma Rafa da ke kusa da iyaka da Isra'ila da kuma Zirin Gaza na Falastinu, ya bada damar kama wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci a kalla 229 tare da lalata mabuyarsu 85.