sakamakon zaɓen Italia ya tabattar da rinjayen Romano Prodi
April 20, 2006Talla
Bayan bayyana sakamakon zaɓen yan majalisun dokokin ƙasar Italia, har ya zuwa sahiyar yau, Praminista mai barin gado, Silvio Berlusconi, ya ƙi amincewa da kayin da ya sha.
A nasa ɓangare, tunni, shugaban rukunin jam´iyun adawa, da su ka samu rinjaye a wannan zaɓe, wato Romano Prodi, ya fara shirye shiryen girka sabuwar gwamnati.
Ya kuma bayyana babban aikin da ke gaban sa, a halin yanzu
Masu kulla da harakokin siyasa a ƙasar Italia, sun nunar da cewa, Romano Prodi, zai gudanar da mulki cikin yanayi mai wahala, ta la´akari da cewa, rinjayen da ya samu dan ƙwarya ƙwarya ne.