1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Brazil

October 4, 2010

Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu a Brazil.

Shugaba mai barin gado, Luiz Inacio Lula da Silva.Hoto: AP

A ranar 31 ga watan Oktoban nan ne 'yan ƙasar Brazil za su gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban ƙasar, bayan da sakamakon zagayen farko ya nuna cewar, babu ɗan takarar da ya samu rinjaye - mai ƙarfi.

Bayan ƙidaya sakamakon zagaye na farko na zaɓen shugaba ƙasar Brazil, hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da gudanar da zagaye na biyu a ranar 31 ga watan Oktoba - idan Allah ya kaimu.

Shugaban hukumar, Enrique Ricardo Lewandowski, shi ne ya bayyana hakan bayan ƙidayar: Ya ce: "Tuni za mu iya tabbatar da cewar za a je zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa."

Dilma RousseffHoto: AP

'Yar takarar da shugaban ƙasar mai barin gado, Luiz Inacio Lula da Silva ke goyon bayanta, kana babbar jami'a a fadar shugaban ƙasar, Dilma Rousseff ta gaza samun yawan ƙuri'un da zai sa a kauce wa zuwa zagaye na biyu na zaɓen , domin kuwa ta sami kashi 47 cikin 100 ne a yayin da ɗan takarar da ke rufa mata baya a yawan ƙuri,u wanda kuma tsohon gwamnan jihar Sao Paulo ne, Jose Serra ya sami kashi 33 cikin 100 na adadin ƙuri'un da masu zabe suka jefa.

Sai dai tsarin mulkin ƙasar ta Brazil ya tanadi cewar, tilas ne ɗan takara ya sami abin da ya ɗara kashi 50 cikin 100 tukuna ya zama wanda ya sami rinjayen da zai sa a kauce wa shiga zagaye na biyu na zaɓen, wanda a wannan karon kuma, ita Dilma Rousseff ta gaza samu- abin da wasu manazarta ke dangantawa da ra'ayinta akan batun zubar da ciki- ra'ayin da kuma wasu ƙungiyoyin addinin Kirista basu ji daɗinsa ba. A lokacin da take yi wa magoya bayanta jawabi bayan bayyana sakamakon, 'yar takarar da ke kan gaba, Dilma Rousseff cewa ta yi, babban abin da ke gabanta a yanzu, shi ne faɗaɗa tattaunawa tare da ƙungiyoyi daban-daban. Ta ce: "Mun tabbatar da cewar, a lokacin zagaye na biyu, za mu sami muhimmin shirin fayyace wa jama'a batutuwa daban-daban, zamu gana da 'yan ƙasa, mu tattauna da ƙungiyoyi, kana mu yi musayar yawu tare da wakilan ƙungiyoyi masu zaman kansu, waɗanda ko ma dai akan wani dalili ne suke buƙatar yin tattaunawa da mu."

Marina SilvaHoto: AP

A yanzu dai 'yar takarar jam'iyyar The Greens, da ke fafutukar kare muhalli, wadda kuma tsohuwar ministar kula da harkokin muhalli ce a ƙarƙashin gwamnatin shugaba mai barin gado Lula da Silva, da ta zo ta ukku a zaɓen da kashi 19 cikin 100 ita ce za ta iya taka rawa wajen tallafa wa ɗan takarar da zai yi nasara a zagaye na biyu. Marina Silva ta shaida wa magoya bayanta cewar, za ta je zagaye na biyun ne da kuzari da kuma ƙarfin-gwiwa, domin a cewarta, za ta sami damar tsara shawarwarinta.

Jam'iyyar shugaban Lula ta sami ƙarin kujeru shidda a majalisar dattijan ƙasar. A ƙarƙashin jagorancin shugaba Lula da Silva dai, tattalin arziƙin Brazil ya sami ci-gaba kwarai, inda ta ƙara yawan kayayyakin da take safarar su zuwa ƙetare, kana da aiwatar da shirin rage talauci, ko da yake shi ma tsohon gwamnan jihar Sao Paulo da ya zo na biyu, an sami ci-gaba sosai a lokacin da ya ke jagorancin jihar tasa.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas