1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar DRC

November 15, 2006

Hukumar zaɓe mai zaman kanta, a Jamahuriya Demokaradiyar kongo, ta kammala tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2.

Cibiyoyin ƙidayar ƙuri´u 169, a fadin ƙasar baki ɗaya sun bada sakamakon su.

Shugaban ƙasa mai ci yanzu, Joseph kabila, ya sa mu kashi 58, bisa 100 ,na jimilar ƙuri´un da ka kaɗa, a yayin da abokin hamayar sa, Jean Pierre Bemba, ya tashi da kashi 42 bisa 100.

Kimanin kashi 65 bisa ɗari na al´ummar da ya cencenta su yi zaɓe su ka kaɗa ƙuri´un su.

A yayin da yake bayyana sakamakon, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, Apolinaire Malu-Malu ya yi kira ga yan siyasa.

Shima shugaban ƙasa, da ya lashe zaɓen ya yi kiran jama´a ta kwantar da hankulla, to saidai a halin da ake ciki ƙasar na shirin faɗawa cikin wani saban rikici, domin Jean Pierre Bemba, ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, wanda ya ce an tabka maguɗi a cikin sa.