1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen 'yan majalisa a Masar

December 4, 2011

Jam´iyu masu kishin addini sun samu gagaramin rinjaye a zaɓen 'yan majalisar dokokin Masar

Tutar jam'iyar 'yan uwa musulmi

Hukumar zaɓe a ƙasar Masar ta bayyana sakamakon zaɓen 'yan majalisar dokoki.

Jam'iyar PLJ ta 'yan uwa muslumi ta samu kashi kusan 37 cikin ɗari a yayin da jam'iyar Annur ta 'yan Salafiya ta tashi da kashi 24 cikin dari.

A jimilce jam'iyun biyu masu kishin addinin Islama sun sami rinjaye tare da kashi 65 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kada.

Wannan zaɓe ya nuna babban koma bayan ga jam'iyun da babu ruwan su da addini.

A Litinin shida ga watan Disemba za a fara zagaye na biyu na zaɓen 'yan majalisar.

Akwai alamun fafatawa mai zafi tsakanin jam'iyar 'yan uwa musulmi da ta 'yan Salafiya, wanda suka ba da mamaki a wannan zaɓe.

Wannan gagaramar nasara da masu kishin addinin suka samu ta fara tayar da hankalin wasu 'yan siyasar ƙasar Masar da ma na ƙetare, to amma Issam al Eryan, mataimakin shugaban jam'iyar PLJ ya ba da amsa ya na mai cewa:

" Tun lokacin Mubarak wasu ke shakkun demokraɗiya. Ita kuwa demokraɗiya zaɓi ne na jama'a, kuma tilas a mutunta wannan zaɓi. Bukatarmu ita ce a haɗa kai domin ƙasa ta ci gaba"

Ranar 10 ga wata Janairu hukumar zaɓen zata bayyana sakamakon ƙarshe na 'yan majalisar dokoki. Sannan kuma ta shiga shirye-shiryen zaɓen 'yan majalisar wakilai.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal