1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe da ya sauya siyasar Angela Merkel

Mouhamadou Awal Balarabe YB
October 29, 2018

Koma baya da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta samu a zaben 'yan majalisa na jihar Hessen ya bar baya da kura a gwamnatin tarayya, inda Merkel ta yanke shawarar wanke hannayenta daga harkokin siyasa bayan wa'adinta.

Berlin Merkel-Pressekonferenz nach Hessen-Wahl
Hoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Batun bude kofa ga 'yan gudun hijira da rikicin shugabanci tsakaninta da ministan cikin gidan Jamus na daga cikin abubuwa da suka shafa wa Angela Merkel kashin kaji.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yada kwallon ne sakamakon sha da kyar da jam'iyyarta ta CDU ta yi a zabuka biyu da suka gudana cikin makonni biyu. Hasali ma jihohin na Bayern a kudanci da kuma Hessen a tsakiyar kasar na daga cikin wadanda jam'iyyarta ta CDU ke da karfin fada a ji, amma kuma alkiblar da gwamnati ta dosa ta jefa ta cikin hali na tsaka mai wuya. Saboda haka ne Merkel ke kokarin kare kanta da jam'iyyarta da ma gwamnatin hadaka domin kada ruwan rikicin siyasa da ake fama da shi ya yi awon gaba da su, inda a taron manema labarai da ta shirya a Berlin ta yi alkawarin cewar tana kan hanyar raba gari da siyasa kwata-kwata.

Angela Merkel da Friedrich Merz a wani taro a Berlin shekarar 2003Hoto: Imago/photothek

"A babban taron CDU na gaba na watan Disamba a Hamburg, ba zan sake tsayawa takarar mukamin shugabar CDU ta Jamus ba, na biyu, wannan wa'adi na hudu shi ne na karshe da zan yi a matsayin shugabar gwamnatin Tarayya Jamus. A zabukan 'yan majalisa na 2021 ba zan sake zama 'yar takarar Jam'iyyar ba, kuma ba zan sake komawa majalisar ba, Ina so in sanya wannan a cikin kundin cewar ba zan sake neman matsayi na siyasa ba. " A cewar Angela Merkel.

Alal hakika ma dai koma bayan da jam'iyyar ta masu matsakaicin ra'ayin gurguzu ta samu ta zarta ta CDU ta Merkel. Sai dai Andrea Nahles shugabar jam'iyyar SPD ta ce kawancen na nan daram-dakam.

Shugabar gwamnatin Jamus ba ta zabi wanda ta so ya gajeta a mukamin shugaban jam'iyyar CDU ba, amma tuni babbar magatakadar jam'iyyar Annegret Kramp-Karrenbauer da kuma ministan kiwon lafiya Jens Spahn da Friedrich Merz wanda shi ne ke adawa da manufofin Merkel suka bayyana aniyar tsayawa takara.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani