1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Guinea

Suleiman Babayo
October 24, 2020

A kasar Guinea Conakry da ke yankin yammacin Afirka, hukumar zabe ta bayyana Shugaba Alpha Conde, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar lamarin da ya bar baya da kura.

Guinea Präsidentschaftswahlen | Alpha Conde
Hoto: John Wessels/AFP

A kasar Guinea Conakry da ke yankin yammacin Afirka, hukumar zabe ta bayyana Shugaba Alpha Conde, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya gudana a makon jiya, lamarin da ya bar baya da kura.

Wannan sakamako yana cike da rudani da rashin amincewa daga 'yan adawa a kasar da aka saba ganin tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa. Shugaban hukumar zaben Kabinet Cisse ya ayyana sakamakon:

"Karkashin doka mai lamba 41 na kundin tsarin mulki, wadda ke cewa dole shugaban kasa ya samu kuri'u mafi rinjaye da aka kada, inda duk dan takara da ya samu yawan kuri'un da ake bukata za a ayyana a mastayin wanda ya lashe zabe. Bisa haka dan takara Alpha Conde na jam'iyyar Rally of Guinean People ya lashe zaben shugaban kasa a zagye na farko da kuri'u kashi 59.49 cikin 100."

Hoto: John Wessels/AFP

Ana sanar da sakamakon zaben magoya bayan Shugaba Alpha Conde suka shiga murna. Hukumar zaben ta Guinea ta kuma ce babban abokin hamayyar Shugaba Conde, Cellou Dalein Diallo, ya samu kashi 33.5% na kuri'un. Tuni jagoran 'yan adawa Diallo ya ce zai kalubalanci wannan sakamakon zaben tare da neman magoya baya kan kan zanga-zanga.

Tun farko jagoran 'yan adawa Cellou Dalein Diallo, ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben. Shi dai Shugaba Alpha Conde mai shekaru 82, ya shafe shekaru 10 kan madafun iko, kuma ya yi gyara ga kundin tsarin mulkin domin sake samun wani sabon wa'adi.

Rahotanni daga kasar ta Guinea Conakry da ke yankin yammacin Afirka na cewa ana zaman dar-dar a bayan sanar da sakamakon da hukumar zabe ta yi.