1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben majalisar dokokin Afghanistan

November 13, 2005

Jami´an sa ido a zaben sun nunar da cewa bisa ga dukkan alamu shugaba Ahmed Karzai na Afghanistan zai samu rinjayen da yake bukata a majalisar dokokin kasar. Wakilan kungiyoyi masu zaman kansu a birnin Kabul sun ce bangaren shugaba Karzai zai samu kimanin kashi 60 cikin 100 na yawan kujeru a sabuwar majalisar dokokin. To sai dai ba za´a fayyace irin alkiblar siyasa da sabuwar majalisar wakilan zata dauka domin ´yan takara masu zaman kansu kadai aka amince su shiga cikin majalisar amma ba kungiyoyi ko jam´iyu ba. Sanarwar da hukumar zaben kasar ta bayar ta ce kusan kashi 50 cikin 100 na kujerun majalisar 249 zasu kasance a hannun shugabannin kabilu ko kuma tsofaffin madugan ´yan tawaye. Hatta wasu tsofaffin ´ya´yan kungiyar Taliban sun samu wakilci a cikin majalisar. A jiya asabar aka bayyana sakamakon zaben wanda ya gudana watanni biyu da suka wuce.