1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Marco Rubio na Amurka ya fara rangadi a Isra'ila

Binta Aliyu Zurmi
September 14, 2025

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fara wata ziyarar aiki a kasar Isra'ila, bayan mumunan harin dakarun IDF a kasar Qatar.

Ecuador Quito 2025 | US-Außenminister Marco Rubio besucht Ecuador
Hoto: Jacquelyn Martin/AP Photo/picture alliance

Ziyarar na zuwa ne bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya tsawatar wa Isra'ila kan harin data kai kan shugabannin Hamas da ke taro a birnin Doha a wannan makon.

Wannan dai shi ne karon farko da Isra'ila ta kai irin wannan hari kan kawayen Amurka na Qatar, kuma ya kara sanya wani sabon matsin lamba a yunkurin diflomasiyya na ganin an cimma matsaya a Gaza da yaki ya daidaita.

Kafin ya tashi zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, Rubio ya shaida wa manema labarai cewa, ko da yake Trump bai ji dadin harin Isra'ila a Qatar ba amma hakan ba zai canza komai a dangantakarsu ba.

Mista Rubio ya kara da cewar Amurka da Isra'ila zasu sake tattaunawa a kan tasirin Isra'ila na yunkurin tsagaita wuta.

Karin Bayani:Gaza: An gabatar wa Hamas sabon daftarin yarjejeniyar tsagaiata wuta 
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW