1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren MDD zai gana da Zelensky

March 8, 2023

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres zai gana da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a birnin Kyiv kan batun fitar da abinci daga kasar.

Ukraine-Krieg Kiew | UN-Generalsekretär Antonio Guterres  und Präsident Selenskyj
Hoto: Ukrainian Presidential Press/PA/dpa/picture alliance

Wannan dai na kasancewa karo na uku da sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ke kai ziyara Ukraine tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a kasar shekara guda da ta gabata. Ganawar bangarorin biyu za ta mayar da hankali kan batun ci-gaba da fitar da hatsi daga Ukraine karkashin shirin nan na fitar da abinci zuwa wasu kasashen duniya. Wani kakakin sakataren Majalisa Dinkin Duniyar Farhan Haq, ya ce za a bayar da bayanai kan yadda tattaunawar ta kasance a nan gaba. 

Yayin ziyarar ta Guterres, ana sa ran sabunta yarjejeniya da aka cimma tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Turkiyya a watan Julin shekarar da ta gabata na fitar da hatsin Ukraine zuwa kasuwannin duniya ta tekun Bahar Aswad, wanda hakan ya taimaka wajen rage hauhawan farashin kayan abinci da ya jefa kasashe masu tasowa cikin barazanar yunwa.