Sabon sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio na ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu da Amurkan ke son karbe iko da shi.
Sakataren wajen Amurka Marco Rubio da firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: U.S. Embassy Jerus/dpa/picture alliance
Talla
Biyo bayan bayyana shirinsa na karbe ikon da yankin Zirin Gaza na Falasdinun da shugaban Amurka Donald Trump yayi, sabon sakataren harkoin wajen na Amurkan Marco Rubio ya isa yankin Gabas Ta Tsakiya a kokarinsa na tallata shirin da ke shan kakkausar suka daga kasashen yankin da ma sauran kasashen duniya. Rubio ya fara ziyarar tasa ne dai daga Isra'ila tare da rakiyar miyagun makamai masu linzami sanfurin MK-84 da gwamnatin Biden ta ki bai wa Tel Avivi din a baya, saboda damuwa game da tasirin da za su yi a yankunan da ke da yawan jama'a a Zirin Gaza.
Dubban mutane na komawa Arewacin Gaza
Duk da gargadin da sojojin Isra'ila suka yi, dubban Falasdinawa da aka yi wa kawanya sun yi tattaki daga Kudu domin komawa arewacin Zirin Gaza.
Hoto: Ramadan Abed /REUTERS
Hijira daga Kudu zuwa Arewa
Dubban Falasdinawa sun yi tattaki ta gabar teku daga kudu zuwa arewacin Zirin Gaza. Sun dauki wannan mataki duk da cewa sojojin Isra'ila sun yi gargadin cewa har yanzu yankin Arewa na zama yankin da ake gwabza fada. Sai dai fatan janyewar sojoji a Arewa da fargabar kai farmakin soja a kudancin kasar ya sa su komawa gidajensu, duk da cewa an lalata su.
Hoto: Yasser Qudihe/Middle East Images/IMAGO
Yankunan da aka lalata
Yankuna da dama na Zirin Gaza ne sojojin Isra'ila suka lalata don mayar da martani ga mummunan harin ta'addancin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Kusan rabin al'ummar yankin miliyan 2.3 sun guje wa fadan zuwa kudancin zirin. Amma da yawa sun fara komawa Khan Yunis, inda gine-gine da yawa suka lalace.
Hoto: Ali Jadallah/Anadolu/picture alliance
Takardun gargadi
Sojojin Isra'ila sun rarraba takardu domin yin gargadi ga mutane cikin harshen Larabci game da "yanki mai hatsari na yaki" a arewacin Gaza. Wasu iyalai da suka koma Beit Hanoun da Jabalia a makonnin da suka gabata, bayan janyewar sojojin Isra'ila, sun sake barin wurin saboda fargabar barkewar wani sabon fada.
Hoto: -/AFP/Getty Images
"Muna son gidajenmu"
Tun tsawon watanni, wadanda suka rasa matsugunansu suna zama a karkashin tantuna a sansanoni da makarantu da kuma gidajen dangi a kudancin Zirin Gaza. "Muna son gidajenmu, muna son rayukanmu, muna so mu koma, ko ba a tsagaita wuta ba," in ji wata mace da ake kira Ummu Nidhal Khatab a kan hanyarta ta komawa Arewacin Zirin Gaza.
Hoto: Yasser Qudihe/Middle East Images/IMAGO
Wahala, 'yunwa da rashin isasshen taimako
Halin da ake ciki na jin kai a Zirin Gaza yana da muni. Bayan watanni shida na yaki, kusan mutane miliyan daya na fama da 'yunwa. Akwai fatan cewa kayan agajin da ake harbawa ta sama za su iya rage wahalhalun da ke addabar arewacin zirin, sannan Isra'ila ta bude sabbin hanyoyin kai kayan agaji. Sai dai a cewar Majalisar Dinkin Duniya, yawancin kayan agajin ba sa kaiwa ga mutanen da ke bukata.
Hoto: Mahmoud Issa/dpa/picture alliance
Harbe-harbe a wani shingen bincike
Tafiya zuwa arewacin Zirin Gaza na da hadari. Shaidun gani da ido sun sanar da cewa, an yi harbe-harbe a wani shingen bincike da sojojin Isra'ila ke da iko a hanyar shiga yankunan arewaci. Asibitin Awda da ke tsakiyar Zirin Gaza ya ba da rahoton mutuwar mutane biyar tare da jikkatar wasu 54. Sojojin Isra'ila ba su ce komai kan wannan batu ba.
Hoto: Ramadan Abed /REUTERS
Mage a cikin jaka
Wani yaro ya kula da kyanwarsa a kan hanya mai hadari ta zuwa Arewacin Gaza. Yakin ya riga ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula Falasdinawa sama da 34,000, kuma akalla 13,000 daga cikinsu yara ne. Kimanin mutane miliyan 1.8 sun rasa matsugunansu. Gagarumar matsalar jin kai na shirin kunno kai, a daidai lokacin da wasu sassan yankin ke fuskantar yunwa. Ba a kai ga yarjejeniyar tsagaita wuta ba.
Hoto: Ramadan Abed/REUTERS
Hotuna 71 | 7
A yayin ganawarsa da firaministan Isra'ilan Benjamin Natenyahu a birnin Kudus da Trump a wa'adin mulkinsa na farko ya ayyana shi a matsayin fadar mulkin Isra'ila ita kadai har abada, Mista Rubion ya nuna cikakken goyan bayansa ga dukkanin matakan da ya ce Isra'ilan na dauka domin kare tsaronta. Ya jaddada cewa yana ziyara a yankin ne, domin tabbatar da ganin an sako 'yan Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su cikin gaggawa da kuma tallata sabon shirin warware rikicin Gabas ta Tsakiyar da Shugaba Trump ya yi ta maza wajen bayyana shi ba tare da wata kumbiya-kumbiya ba. A nasa bangaren firaministan Isra'ilan ya ce yana aiki tukuru, domin tabbatar da shirin shugaban Amurkan Donald Trump na kwashe al'ummar Falasdinawa daga Zirin Gaza, tare da yabon Trump din kan hallacin da ya ce yana nunawa al'ummar Isra'ilaan.
Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta
02:06
This browser does not support the video element.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Masar ke jagorantar Larabawa wajen gabatar wa Amurka da ma duniya wani sabon kudirin sake gina Zirin Gaza ba tare da an kori mazauna yankin ba, kudirin da ke cin karo da na Shugaba Trump din da ke fuskantar mummunar turjiya daga kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya da mukamai. Suna dai siffanta shirin na Trump da kokarin tabbatarwa Isra'ila manufofinta da ta kasa cimma duk da gwabza yakin watanni 15, a yanzu ake kokarin amfani da Kasashen na Larabawa da ke tsoron gaba-gadi irin na Trump din domin aiwatar da shi ta bayan fage. Tuni dai da ma kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta nuna goyan bayanta ga shirin korar mazauna ynakin Zirin Gazan, inda aka jiyo ma'aikatar harkokin wajenta na cewa ba ta zaton ya zuwa yanzu akwai wani kudiri mafi gamsarwa kan makomar Gaza fiye da wanda Trump din ya gabatar.