Libiya: Hada-hadar man fetur ta dawo
July 10, 2020Talla
Ma'aikatar man fetur din kasar ta Libiya ta sanar da cewa tuni wani jirgin ruwan dakon danyen man da ya kamata ya soma aikin jigilar man ya dire a gabar tekun al-Sedra mai albarkatun danyen mai a yankin gabashin kasar.
Sai dai rahotanni sun ce duk da sake dawowa da hada-hadar aikin danyen man, kasar ta Libiya za ta shafe tsawon lokaci kafin ta kai ga samar da ganga miliyan daya da digo biyu na danyen mai a kowace rana kamar yadda aka saba, duba da mummunar illa da ma koma bayan da kamfanin hakar man fetur din kasar ya fuskanta sakamakon tashe-tashen hankulan.