Bude makarantu a Saliyo
February 4, 2015Talla
Makarantun na Saliyo dai sun kwashe tsahon watanni bakwai a rufe sakamakon barkewar annobar cutar ta Ebola mai saurin kisa a yankin yammacin Afirka. Gwamnatin ta Saliyo ta dauki matakin rufe makarantun ne domin dakile yaduwar cutar ta Ebola wadda ake saurin daukarta ta hanyar cudanyar jama'a. Tun a watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2014 ne dai mahukuntan na Saliyo suka sanya dokar ta baci a kasar biyo bayan barkewar cutar wadda ta hallaka akalla mutane 9,000 a yankin yammacin Afirka kuma 3,000 daga cikinsu 'yan kasar ta Saliyo ne.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu