1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake dage zaben shugaban kasar Somaliya

Abdullahi Tanko Bala
December 27, 2016

Hukumomi a Somaliya sun sake dage zaben shugaban kasar a karo na hudu sakamakon zarge-zargen magudi da kuma barazana ta fuskar tsaro. Dukkan masu ruwa da tsaki dai amince da jinkirta zaben zuwa Janairu mai kamawa.

Bildergalerie Grün in Afrika
Hoto: AFP/Getty Images

Kasar ta da ke yankin kusurwar Afirka dai na fama da rikicin hauloli da kuma barazanar kungiyar al Shabbab mai tsatsaurar akida wadda kuma har ila yau ta ke adawa da tafarkin dimokradiyya irin na yammacin Turai. A waje daya dai 'yan adawa sun baiyana damuwa da yawaitar dage zaben, suna masu cewa tsarin zaben na cike da magudi da nuna fifiko ga wani bangare inda wasu ke zama 'yan mowa wasu kuma 'yan bora.

Zaben na bana dai shi ne na biyu da za'a gudanar bisa tafarkin dimokradiyya a kasar ta Somaliya tun bayan da aka hambarar da gwamnatin mulkin kama karya ta Mohammed Siad Barre shekarar 1991. A zaben da aka gudanar a shekarar 2012, wakilai 135 aka zaba na majalisar wakilai. Sai dai a wannan karo da za'a zabi 'yan majalisu biyu wato majalisar wakilai da ta dattijai, inda za a zabi wakilai ne1400 wanda su ne kuma za su zabi shugaban kasa.

Fadumo Dayib ce mace ta farko da ta fara neman kujerar shugabancin kasa a SomaliyaHoto: Harvard University/Stephanie Mitchell

Dalilai da dama da suka sanya dage zaben na 2016 dai sun hada da zabin cancantar wakilai bisa zargin bada toshiya da cin hanci da sayen kuri'u da ma yin barazana a wasu lokutan lamarin da wakilin Majalisar Dinkin Duniyar a Somaliya ya ce abin dubawa ne. A yanzu dai an shirya 'yan majalisar za su zabi shugaban kasa a ranar 20 ga watan janairu kuma 'yan takara 20 ne ke neman mukamin shugabancin kasar cikinsu har da  Fadumo Dayib mace ta farko a tarihin Somaliya da ke son darewa kujerar shugaban kasar. Fadumo dai ta ce makasudin yin wannan takara da ta ke bai wuci kawo sauyi ga tsarin yadda al'amura ke gudana a Somaliya ba.

Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na son neman wani sabon wa'adin mulkiHoto: Reuters/M. Dalder

A wannan takara dai shugaban mai ci Hassan Sheikh Mohammed na jam'iyyar zaman lafiya da gina kasa da kuma Firaminista Omar Abdulrashid Ali Sharmarke wanda aka zabe shi ba a karkashin kowace jam'iyya ba su ne ake kallo a matsayin wadanda suka fi farin jini a zaben. Tsarin hauloli na da matukar tasiri a zaben kasar Somaliya. Shugaban kasar dai ya fito ne daga kabilar Hawiye kuma ya na fatan daukaka Somaliya a idanun duniya da kuma samun tagomashi na asusun bada lamuni na duniya. Sai dai kuma ya gaza shawo kan tada kayar baya ta 'yan al Shabaab. 

Babban mai kalubalantarsa wato Firaminista Omar Abdulrashid Ali Shermarke wanda aka kashe mahaifinsa a shekarar 1969 da kuma har yanzu ake begensa masanin tattalin arziki ne wanda kuma ke da takardar zama dan kasa na Kanada.Shi dai Shermarke ya fito ne daga kabila ta biyu mafi girma a Somaliya wato kabilar Darod. Babu shakka raba mukamai tsakanin shugaban kasar da Firaminista da kuma mukami mai karfi na shugaban majalisar dokoki zai zama dambarwa mai karfi a siyasar, sai dai lokaci ne kawai zai nuna yadda zaben zai kasance.