1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Sauya tsarin mulki na yawan shekaru a Chadi

Abdourahamane Hassane
September 15, 2025

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar wanda ya kara wa'adin shugabancin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai ba tare da takaita sabunta wa'adi ba. ´

'Yan majalisar dokokin Chadi
'Yan majalisar dokokin ChadiHoto: Blaise Dariustone/DW

 ´

Kudirin wanda jamiyyar dake yin mulki  ta MPS ta gabatar da shi, daman ta sha yin  kwaskwarima ga wasu tanade-tanade na kundin tsarin mulkin kasar Chadi na ranar 29 ga Disamba, na 2023.

Wakilan majalisar sun amince da daftarin da gagarumin rinjaye tare da kuri'u  171 yayin da daya ya hau kujerar naki.

Har yanzu ana bukatar a aika daftarin kudirin a  majalisar dattawa kafin kada kuri'a ta karshe a majalisar da aka shirya yi a ranar 13 ga Oktoba,na wannan shekara,  inda za a bukaci kashi uku bisa biyar don aiwatar da wannan gyara ga babbar doka.