1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake nazarin matakin tallafi

Ubale Musa USU/SB
July 19, 2023

Gwamnatin Najeriya za ta sake nazarin shirin tallafa wa iyalai miliyan 12 da Naira 8,000 har na tsawon watanni shida. Wannan dai lamari ne da wasu a kasar ke ganin kamar yana kama da rawan 'yan mata na gaba ya koma baya.

Najeriya | Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na NajeriyaHoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Kama daga masu kwadago zuwa ga kungiyoyi na fararen hula dai ga duk alamu auren zoben da ke tsakanin sabbabin 'yan mulki na kasar da ragowar jama'ar cikin gari na nuna alamun tsami. Tun ba a kai ga ko'ina ba dai miliyoyin 'yan kasar suka sa kafa suka yi fatali da batun tallafawa talakan da ke da burin kashe kudi amma kuma ba tare da iya kai wa ya zuwa tasirin da Abuja ke fatan ta gani ba. To sai dai kuma daga dukka na alamu masu mulkin kasar suna shirin mika wuya bisa karuwar harin da ke zaman mai girma kuma na iya kai wa ya zuwa sabon rikici cikin kasar a nan gaba.

Karin Bayani: Najeriya za ta ciwo bashi

Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu dai ya ce ko bayan dubu 8,000 akwai kuma nau'o'i na tallafin daban-daban da suka hada da abinci da takin zamani ga mutane miliyan 50 ko kuma daya a cikin kowane dan kasar guda hudu.

Magoya bayan sabon shugaban NajeriyaHoto: DW

Sake takun rawa a bangaren masu rike da madafun ikon kasar dai daga duk alamu na zaman aiken sako bisa inda kasar take shiri ta karkata a tsakanin talakawan da ke fadin suna da bukatar sauki da gwamnatin da ke shirin tara kudi. Auwal Musa Rafsanjani dai na zaman jigo a kungiyoyi na farafren hula ta kasar da kuma suka daukilokaci suna karatu na tatsine a cikin tsarin da yace yana da babban burin kudin dare daya ga wasu.

Bara'a da tallafin ko kuma kokari na wa-ka-ci ka tashi, sake kara farashin man a cikin sabon tsarin dai na kara tayar da hankula cikin kasar da ke dada kallon babu. Sama da mutane miliyan 130 ne dai ke da bukatar tallafi a Najeriya kasar da ke dada kallon karuwa ta talauci, yanzu haka. Kuma ra'ayi yana rabe ko a tsakanin kwarraru bisa hanyar tunkarar annobar ta talauci da ke zaman ruwan dare cikin kasar a halin yanzu.

Dr Hamisu Yau dai na zaman kwarrare ga tattali na arzikin kasar da kuma ya ce akwai alamun rudani ga kamun ludayin sabuwar gwamnatin kasar. Rudani cikin kasa ko kuma neman mafitar ta'azzara ta talauci, mai da hankali ga abinci a tunanin kungiyar kare, muradun arewacin kasar ACF na zaman na kan gaba maimakon dubu takwas da ba ta da tasiri a kokari na kare talaucin.