1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a sake zaben gwamna a Jihar Imo

Muhammad Bello AH
November 8, 2023

Kungiyar kwadago ta kasa ta NLC ta umarci tsindima yajin aikin ma'aikata a fadin jihar Imo yayin da ake shirin shiga zaben gwamna a cikin kwanaki uku ma su zuwa a Jihar.

Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

 Sharhi kan sakamakon zaben Najeriya bayan dai rashin cimma yarjejeniya ta samun kwanciyar hankali yayin gudanar da zaben na gwamnan a jihar ta Imo, da dama an matsa lambar a jihar rikice rikice,sai kuma kwatsam kungiyar kwadagon kasar ta NLC, ta ayyana tsindima yajin aikin ma'aikatan jIhar ta ImO, wadda kuma zai fadada zuwa sassan kasar 'yan kwanaki ma su zuwa, kuma NLC ta ce ba ruwanta da  wani zabe da za a yi.

Zaben gwamna tafe da yajin aikin ma'aikata a kudancin Najeriya

Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

 A Jihar Bayelsa ma dai a yankin kudu maso kudun Najeriya, shirye-shirye sun kankama na zaben na gwamna, da a ke ganin za a fafata da gwamna mai neman wa'adi na biyu, wato Douye Diri na jam'iyyar PDP,da kuma tsohon ministan mai da dama ya taba yin gwamna a jihar wa'adi na daya, wato Timipre Sylva na jam'iyyar APC. Haka kuma akwai sa hannun tsohon shugaban Najeriya Good Luck Jonathan cikin harkokin zaben jihar ta Bayelsa, da a ka nunar ya na goyon bayan gwamna da ke kan gado  Douye Diri.