1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakin Strauss-Kahn na IMF

Halimatu AbbasMay 21, 2011

An ba da beli ga tsohon shugaban IMF, Dominique Strauss-Kahn bayan da aka shafe kwanaki biyar ana tsare da shi bisa yunƙurin yi wa wata ma'aikaciyar otel fyaɗe. Za a kuma ci gaba da tsare shi a gidansa.

Dominique Strauss-Kahn(ta dama) tare da lauyansa.Hoto: AP

An saki tsohon shugaban asusun IMF, duniya Dominique Strauss-Kahn bayan da aka shafe kawanaki biyar ana tsare da shi bisa zargin da ake masa na cewa yayi yunkurin yi wa wata mace fyaɗe.To ama za a ci gaba sa da tsare shi a gidansa. An miƙa Strauss-Kahn ne ga wata ma'aikatar tsaro mai zaman kanta da ta ɗauke shi zuwa gidansa da ke garin Manhattan. Lauyoyinsa sun aike da dala miliyan guda na beli da kuma dala miliyan biyar a matsyin tabbaci. Ana zargin Strauss-Kahn ne da yunƙurin yi wa wata ma'aikaciyar Otel fyaɗe -zargin da ya musunta. A dai halin yanzu ana ci gaba da tafka muhawara a faɗin duniya game da wanda zai gaje shi bayan da yayi murabus daga mukaminsa na shugaban asusun. A ranar 20 ga watan Mayu asusun na IMF ya ce a ranar Litinin 23 ga watan Mayu ne zai fara karɓar sunayen waɗanda za su tsaya takarar shugabancin asusun , kuma za aada sabon shugaban ne kafin karshen watan Yuni mai kamawa. Shugbabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta miƙa bukatar sake naɗa wani jami'i na Turai a matsayin shugaban asusun na IMF. To ama a ɗayan bangaren kuma China so take an ba da wannan muƙami ga wani jamii daga wata kasa dake samun ci gaban tattalin arziƙi a cin gaggawa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal