1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Chadi: Sakin Masra zai ba shi damar takara?

August 17, 2026

Matakin sakin 'yan adawa da shugaban Chadi ya dauka na haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan siyasa, a daidai lokacin da wasu 'yan kasar ke maraba da matakin saboda zai taimaka a dinke barakar da ake fama da ita.

Chadi | N'Djamena | 2026 | Mahamat Idriss Déby Itno | Sucès Masra | Adawa
Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Déby ItnoHoto: Daniel Beloumou Olomo/AFP

Afuwar da Shugaba Mahamat Idriss Deby Itino ya yi wa tsohon firaministan Chadi kuma shugaban jam'iyyar Les Transformateurs Succès Masra da kuma wasu jami'ai takwas na gamayyar GCAP ta kawo karshen zamansu a gidan gyaran hali, sai dai ba ta soke hukuncin da kotu ta yanke musu ba. Wannan yana nufin cewar, an sake su daga gidan yari amma tarar kudi da bayanan laifukansu na kunshe a cikin littafin rayuwarsu.

Saki ko Afuwa?

Sannan rashin cancantarsu na tsayawa takara, na nan daram. Mai sharhi kan siyasa Bétinbaye Yamingué ya bayyana cewa, akwai banbamci tsakanin sakin 'yan siyasa da aka yi da ainihin kalmar afuwa a fuskar doka. Majalisar dokokin kasa ce kawai, ke da hurumin zartar da dokar afuwa a Chadi. Amma a inda gizo ke saka shi ne, jam'iyya mai mulki ce ta mamaye majalisar da kujeru 124 daga cikin kujeru 188. Sanar da matakin sakin manyan 'yan adawar Chadin daga kurkuku, ta haifar da martani  mabambanta a kasar.

Madugun adawar kasar Chadi Succès MasraHoto: Issouf Sanogo/AFP

Amma a lokacin da aka tuntube ta, jam'iyyar Les Transformateurs ta Succès Masra ta ki cewa uffan kan batun. Kakakin jam'iyyar ya nuna cewa, zai fi son ya jira a sallami shugabansu daga gidan yari kafin su bayyana matsayarsu. Sai dai mataimakin shugaban jam'iyyar Ndolembai Sadé Njesada da kamfanonin labarai suka ambato ya yi maraba da matakin, inda ya gode wa Shugaba Mahamat Deby. A ganinsa, ya zabi ci gaba da hada kan kasa. Ya kuma bayyana fatansa na shugaban ya bude babin tattaunawa, domin ciyar da zaman lafiya gaba.

Afuwa ko talala?

Amma a nasa bangaren mai magana da yawun gamayyar jam'iyyun GCAP Hissein Abdoulaye ya ki amincewa da wannan sakin da shugaban kasa ya yi wa 'yan adawa, inda ya nemi a yi musu afuwa. A gare shi daure manyan 'yan siyasa sannan a yafe musu 'yan watanni bayan haka yayin da ake ci gaba da kwace hakkinsu na siyasa, ya zama babban koma-baya ga tsarin dimukuradiyya. A bangaren fadar shugaban kasar Chadi kuwa, ra'ayi ya bambanta sosai da na 'yan adawa. Jam'iyyar MPS mai mulki ta yi maraba da shawarar sakin 'yan adawa da ta bayyana a matsayin "mai amfani," kuma wacce za ta ba wadannan manyan 'yan siyasa damar komawa ga iyalansu.

Fassara: Mouhamadou Awal Balarabe

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani