1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Saliyo: Ana tuhumar wasu mutane kan yunkurin juyin mulki

January 3, 2024

A kasar Saliyo, an gurfanar da mutum 12 da ake zargi da laifin cin amanar kasa da kuma wasu laifukan na daban da suka hadar da yunkurin kifar da gwamnati a shekarar da ta gabata 2023.

Shugabar kasar Saliyo Julius Maada Bio
Hoto: Ali Balikci/AA/picture alliance

A kasar Saliyo, an gurfanar da mutum 12 da ake zargi da laifin cin amanar kasa da kuma wasu laifukan na daban da suka hadar da yunkurin kifar da gwamnati a ranar 26 ga watan nuwambar shekarar da ta gabata 2023.

Daga cikin mutunen akwai Amadu Koita, wanda ake zargi da cewa shi ya kitsa yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Koita na daga cikin manyan dogaran tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma, kuma ya yi kaurin suna wajen caccakar gwamnatin shugaba Julius Maada Bio, a shafukan sada zumunta.

An dai cafke shi ne a ranar 4 ga watan disamba 2023, tare da wasu mutanen kimanin 85 da zargin hannu a yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Maada Bio, a watan nuwambar shekarar da ta gabata.

Yunkurin juyin mulkin ya sanya fargaba a kasar da ke yammacin Afrika, kasancewar tuni kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyyar Nijar da kuma Guinea suka fada komar juyin mulki tun daga 2020.